Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Kane, Ramsdale, Pogba, Mbappe, Zouma

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Wakilin Cristiano Ronaldo Jorge Mendes ya gabatar da batun dan gaban na Juventus da Portugal mai shekara 36, ga Manchester City. (Jaridar Corriere dello Sport)

Amma kuma City din ta kafe cewa dan gaban Tottenham, kuma kyaftin din Ingila Harry Kane, mai sheakar 28, har yanzu shi ne ta fi bukata. (Jaridar Mirror)

Asalin hoton, Getty Images

Kane ya gaya wa shugaban Tottenham Daniel Levy cewa ya ki bin yarjejeniyar da aka kulla ta sayar da shi fam miliyan 125 ga Manchester City. (Jaridar Telegraph)

Asalin hoton, Getty Images

Bayan da bai halarci atisaye da kuma wasan da kungiyarsu ta doke City ba, a yanzu Kane zai taka wa Spurs leda a wasansu na gasar Turai ta Europa Conference League, da za su yi da kungiyar Paços de Ferreira ta Portugal ranar Alhamis. (Guardian)

Arsenal ta koma tattaunawa da Sheffield United a kan cinikin mai tsaron raga Aaron Ramsdale, na Ingila mai shekara 23, bayan da kungiyar ta Blades ta rage masa farashi daga fam miliyan 35 zuwa miliyan 24. (The Athletic)

Sai dai kuma shugaban Sheffield United din Slavisa Jokanovic ya yarda cewa Ramsdale ba ya son tafiya Arsenal. (Mirror)

Asalin hoton, Getty Images

Paris St-Germain ba ta fitar da tsammanin nasara sayen dan wasan tsakiya na Faransa ba Paul Pogba, mai shekara 28, daga Manchester United ba da kuma matashi Eduardo Camavinga mai shekara 18 daga Rennes. (L'Equipe)

PSG ba ta da niyyar sayar da dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ga Real Madrid a bazaran nan. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tottenham na duba yuwuwar sayen dan bayan Chelsea Kurt Zouma. Ana kuma alakanta dan wasan na Faransa mai shekara 26 da tafiya West Ham a bazaran nan. (Sky Sports)

Atletico Madrid ta gaya wa Arsenal da Manchester United cewa dan bayanta, dan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30, ban a sayarwa ba ne. (AS)

Asalin hoton, Getty Images

Tafiyar Martin Odegaard zaman dindindin Arsenal, daga Real Madrid na dab da tabbata, yayin da ake ta yada rahotanni cewa, dan wasan na tsakiya mai shekara 22, dan kasar Norway bai yi atisaye da manyan 'yan wasan Real Madrid ba ranar Talata. (The Athletic)

Wolverhampton Wanderers na shirin taya dan wasan gaba na gefe na Valencia, Goncalo Guedes, mai shekara 24, fam miliyan 21. (Birmingham Mail)

Kociyan Newcastle Steve Bruce yana son karbar aron dan wasan tsakiya na Leicester, dan Ingila Hamza Choudhury, mai shekara 23. (Mail)

Asalin hoton, Getty Images

Gwanin dan wasan Everton James Rodriguez ya musanta labarin cewa yana neman tafiya Atletico Madrid, bayan da aka fassara wani rubutu da dan wasan na Colombia mai shekara 30, ya a tuwita da cewa alama ce ta nuna cewa yana son tafiya wajen zakarun na la Liga. (Liverpool Echo)

Kungiyar Watford na dab da cimma yarjejeniyar sayen dan bayan Torino Lyanco, mai shekara 24, a kan fam miliyan 7.5 (Sky Sports)

Watakila dan wasan tsakiya na Manchester United Andreas Pereira, mai shekara 25, na dab da barin Old Trafford ya tafi Flamengo bayan tafiya aron da dan Brazil din ya yi ta yi. (Mirror)