Afghanistan: Shugabannin Taliban sun fara komawa kasar domin kafa gwamnati

Mullah Abdul Ghani Baradar na daya daga cikin mutane hudun da suka kafa Taliban

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mullah Abdul Ghani Baradar na daya daga cikin mutane hudun da suka kafa Taliban

Shugabannin kungiyar Taliban da ke gudun hijira a kasashen waje sun fara komawa Afghanistan domin kafa gwamnati.

Hakan na faruwa ne kwana guda bayan kungiyar ta gudanar da taron manema labaranta na farko tun bayan da ta kwace mulkin kasar.

A wurin taron, mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce suna tattaunawa domin kafa gwamnati a Afghanistan, yana mai cewa tsarin Shari'ar Musulunci za su aiwatar.

Daya daga cikin shugabannin da suka koma kasar shi ne wanda aka kafa kungiyar da shi, Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda ya koma daga Qatar, inda ya shafe watanni yana jagorantar yarjejeniyar ficewar dakarun Amurka daga kasar.

Taron jama'a sun rika kabbara suna maraba da shi a lokacin da aka wuce da shi a mota daga filin jirgin sama na Kandahar, cibiyar kafa kungiyar kuma babbar tungarta.

Kungiyar ta Taliban ta ce a karkashin shugabancinta, mata za su iya karatu da yin aiki, amma bisa tanadin dokokin Musulunci. Sai dai ba a san abin da hakan ke nufi a aikace ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid a taron manema labarai na farko bayan karbe gwamnatin Afghanistan

Mata za su iya samun damar yin zabe, ko rike wani mukami na siyasa? Za su iya zama masu shari'a ko 'yan wasan motsa jiki? Babu wannan amsa zuwa yanzu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko da aka matsa wa kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid a lokacin wani taron manema labarai kan ya bayar da karin bayani a kan wadannan tambayoyi, sai ya nuna cewa sabuwar gwamnati da za ta zo da sabbin dokoki ita ce ke da wannan amsa.

Sai dai ya nuna cewa za a bukaci mata a fannin kula da lafiya da shari'a da ilimi da kuma aikin tabbatar da doka.

Duk da yadda wasu mata da sauran 'yan kasar ke nuna shakku kan batun tabbatar da 'yancin matan da kungiyar ta yi, wasu matan sun yi maraba da abubuwan da kungiyar ke fada.

Wata mata ta ce: ''Idan har za a ba su damar yin aiki da kuma karatu, ai wannan shi ne 'yanci a wurina, wannan ita ce iyaka. Wadda Taliban ba ta tsallaka ba zuwa yanzu...''

Cika alkawari

Komawar shugabannin Afganistan gida na zuwa ne a yayin da Amurka ta ce za ta so ta ga Taliban ta cika alkawarin da ta yi na mutanta 'yancin dan adam kafin ta san yadda za ta yi alaka da gwamnatin kungiyar.

Amurka ta bayyana hakan ne yayin da kuma aka bayar da sanarwar cewa shugabannin kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki, G7 za su gana a makon mai zuwa domin tattaunawa a kan manufa daya kan sabon shugabancin Afghanistan.

Amurka, wadda matakin da shugabanta Joe Biden ya dauka da ake gani ya kai ga halin da Afghanistan ta samu kanta a ciki, ta tsaya ta ga yadda salon mulkin Taliban zai kasance a wannan karon, kafin ta san irin alakar da za ta yi da sabbin shugabannin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Biden ya kafe a kan matsayinsa na janye sojin Amurka wanda ya bayar da kafar da Taliban ta kwace mulki

Bayan wata tattauanawa ta wayar tarho ne, tsakanin Shugaba Biden da kuma Firaministan Birtaniya Boris Johnson, aka bayar da sanarwar cewa shugabannin kungiyar kasashe masu karfin masana'antun ta G7 za su yi taro, amma ba na gaba da gaba ba, a mako mai zuwa domin tattaunawa da daukar matsaya guda a kan yadda alakarsu da shugabancin na kungiyar Taliban a Afghanistan za ta kasance.

Asalin hoton, PA Media

Idan kungiyar ta Taliban ta ki tabbatar da alkawari da ta yi na mutunta 'yancin mata da shugabannin tsohuwar gwamnatin kasar, mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na Amurkar, Jake Sullivan, ya ce daga nan zabi daya kawai da zai rage shi ne sanya wa gwamnatin takunkumi.

Daman tun a yanzu ma gwamantin Biden ta ce ta dakatar da hanyar fitar da kudaden gwamnatin Afghanistan da ke a Amurka, da suka hada da zinare na biliyoyin dala da aka ajiye a wani banki a New York.