Aminu Masari: Abin da ya sa muka ce ƴan Katsina su ɗauki makamai don kare kansu

Aminu Bello Masari
Bayanan hoto,

Gwamna Aminu Bello Masari ya ce matakin zai ƙarfafa tsaro a jihar

Masana harkar tsaro a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da kalaman da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi na bukatar al'ummar jihar da ke fama da matsalar tsaro su nemi makamai domin kare kansu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya umarci al'ummar jihar da ke fama da matsalar tsaro da su nemi makamai domin kare kansu.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai, Abdu Labaran Malumfashi, ya fitar inda gwamnan ya ce tsaro ba aikin gwamnati ba ne kawai - dole ne jama'a su yi hoɓɓasa.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wadannan kalaman ne yayin jajanta wa al'ummar da suka rasa 'yan uwansu a garin Jibia sakamakon take su da wata motar jami'an hana fasa kauri ta yi.

Sai dai masana harkar tsaro irin su Manjo Lawal Galma mai ritaya, wani masanin tsaro a Najeriya na ganin hakan gazawa ce.

A hirarsa da BBC Hausa ya ce, "duk lokacin da ka ji manya na kiraye-kirayen cewa mutane su ɗauki makamai su kare kansu to gazawa ce.

"Idan ka ce a ɗauki makamai to waɗanne irin makamaki kake nufi. Dole idan za ka kare kanka dole makaminka ya fi na masu kawo maka hari ƙarfi."

Ya ce sauƙin abin ma idan gwamnatin ce za ta samar da makaman. Kamar misali bai wa ƴan sa kai taimako na irin makaman da za su fatattaki maharan.

A ganinsa bai wa kowa dama ya mallaki makami tamkar ba da damar bazuwar makamai ne ba bisa ƙa'ida ba.

"Gaskiya ya dai kamata gwamnati ta fara tunanin wata hanyar ta daban amma ba ta bai wa mutane damar ɗaukar makamai ba," ya ƙara da cewa.

Mece ce hujjar gwamnati ta cewa a ɗauki makamai?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Abdu Labaran Malumfashi ya shaida wa BBC cewa gwamnan ya ba da wannan shawarar ce saboda bindigar da masu satar mutane ke ɗauka ce ke ba su ƙarfi don haka su ma mutanen jihar su riƙe makamai don kare kansu.

"Idan mutane suka fara ɗaukar makamai don kare kansu, waɗannan masu satar mutane idan suka san za su zo su sami mutane da tasu bindigar, ba za ma su zo ba.

"Kai ma kanka idan ka san kana da bindigarka ba za ma ka bari barayin nan su iso wurinka ba, daga sun ji ka fara harbi za su koma," in ji shi.

Ya kuma ce "Gwamna na ganin wannan zai kawo ƙarshen ta'addanci a jihar. Ba lallai sai sun riƙe bindiga mai tsada ba, ko ƙananan bindigogi za su iya riƙewa su kare kansu," a cewar sa.

Abdu Labaran Malumfashi ya ce idan al'umar jihar Katsina suka fara riƙe bindigogi don kare kansu, ɓarayin daji da masu garkuwa da mutane za su tsorata su daina kai hare-hare.

Ya kuma bayyana cewa kare kai ya fi ƙarfin komai, duk mai son ya kare kansa zai iya ɗaukar ko wane irin mataki.

Mai bai wa gwamnan shawara ya ce gwamnatin Aminu Bello Masari na ganin cewa wannan shawarar za ta taimaka sosai saboda jami'an tsaro a jihar ba su da yawan da za su iya kare kowa.

"A ƙaramar hukuma guda sai ka ga kauyuka ɗari. To ko da ɗan sanda da soja ɗaiɗai za a kai ba za su isa ba," a cewarsa.

Ya kuma bayyana cewa tsaro ba haƙƙin gwamnati ba ne kawai, haƙƙi ne da ke kan kowa.

Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya kamar Zamfara da Kaduna da ke fama da matsalolin tsaro da suka danganci fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

Yankuna da dama na jihar na ganin hare-hare a kai a kai inda ƴan bindiga ke aukawa ƙauyuka su kashe mutane sannan su yi awon gaba da mata da ƙananan yara tare da satar dabbobi.

A watan Disamban 2020 ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar sakandiren garin Ƙanƙara inda daga baya gwamnati ta ceto su.