Zara Rutherford: Matashiyar da ta fara zagaya duniya a jirgi ita kaɗai

Zara Rutherford climbing into the cockpit of her aircraft while her father looks on

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Zara Rutherford ta tashi ne daga Kortrijk a Belgium

Wata matashiya matuƙiyar jirgin sama ta fara wani ƙoƙari na zama mace ta farko mafi ƙarancin shekaru da za ta zagaye duniya ita kaɗai a jirgi.

Jirgin Zara Rutherford, mai shekara 19, ya ɗaga da misalin ƙarfe 9 saura na safe agogon GMT daga garin Kortrijk a ƙasar Belgium - inda ta yi lattin awa ɗaya saboda yanayi marar kyau.

Za ta shafe wata uku ne tana wannan zagaye.

Ta yi tsayuwar farko a sansanin Popham Airfield a gundumar Hampshire a kudancin Ingila da ƙarfe 10:30 agogon GMT.

Tsohuwar ɗalibar a Makarantar St Swithun da ke Winchester, babban burinta shi ne ta yi shawagi a ƙasashe 52 ta kuma tsallake layin da ya raba duniya na ikweto har sau biyu a yayin bulaguron.

Wacce take riƙe da kambun irin wannan aiki a yanzu haka ita ce Shaesta Waiz, ƴar Amurka, wadda take da shekara 30 a lokacin da ta yi wannan ƙoƙari a shekarar 2017. Shi kuwa namijin da yake kan gaba a wannan lamari ɗan shekara 18 ne.

Shiryen-shiryen Miss Rutherford sun haɗa da horo kan yadda za ta fice daga cikin jirgi idan ya faɗa ruwa - da kuma yadda za ta dinga duba lafiyar jirgin nata.

Tsarin shawagin kuma ya haɗa da tsayuwa 70 da za ta yi da hutu na kwana 19, sannan an tsara za ta kammala ta koma Kortijk ranar 4 ga Nuwamba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Za ta shafe wata uku ne tana wannan zagaye

Miss Rutherford, wacce take zaune a Belgium, ta ce "babban ƙalubalen" zai kasance shiga wurare masu surƙuƙi kamar arewacin Rasha da Greenland.

"Babu mutane sosai da suke zama a can, don haka idan wani abu ya faru zan kasance cikin ruɗu," a cewarta.

Matashiyar, wacce duk zuriyarta matuƙa jirgi ne, ta fara horo ne a lokacin da take ƴar shekara 14 ta kuma samu lasisin tuƙin jirgin sama a shekarar 2020.

Tana tuƙa jirgi samfurin Shark UL - wani irin jirgi mara nauyi mai tsananin gudu.

Za ta yi shawagi zuwa Wick ta Aberdeen, kafin ta bi ta Tekun Atlantika zuwa Iceland da Greenland sai kuma Canada.

Sannan jadawalinta zai kai ta har ƙasan gabashin gaɓar tekun Amurka zuwa kudancin Amurka kafin daga bisani ta cilla zuwa yammacin gaɓar teku zuwa Alaska, ta tsallaka Rasha da gabashi da tsakiyar nahiyar Asiya, kafi ta koma Turai ta hanyar yin ratse a Gabas Ta Tsakiya.

Miss Rutherford ta shafe shekara biyar a Makarantar St Swithun, wacce tana ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin aikin.