Ƙauyuka 9 a jihar Zamfara sun tara wa ƴan bindiga kuɗi

Yan bindiga

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

Ko wane ƙauye an buƙaci ya biya naira dubu ɗari uku

Wasu mutanen ƙayukan jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun tara wa ƴan bindiga kuɗi domin neman samun zaman lafiya da tsira da rayukansu.

Uwayen ƙasa da ke mulkin Dansadau cikin ƙaramar Hukumar Maru ne suka ta tilaswa ƙauyukan yankin biyan kuɗaɗen domin neman zaman lafiya da ƴan fashi sakamakon kashe ɗaya daga cikin ƴan bindiga a yankin, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.

Ya ce an kashe wani ɓarawo ne a kan hanyarsa ta zuwa cin kasuwa, kuma ƴan uwansa sun ce dole sai an biya kuɗin da yake ɗauke da su da ba a gani ba bayan sun tsinci gawarsa.

"An zo an tara talakawa a ƙauyuka tara an ce ko wane ƙauye sai ya biya naira dubu ɗari uku kuma ko wane magidanci sai ya biya," in ji shi.

Ya ce Uban ƙasa ya ce dole sai an biya kudin kafin Asabar, wa'adin da ƴan bindigar suka bayar. "Kuma duk wanda bai biya ba uban ƙasa ya ce a kai mashi shi.

Ɗaya daga cikin shugabannnin yankin, Wazirin masaraurar Dansadau, Mustapha Umar, wanda shi ma ya tabbatar wa BBC da al'amarin ya ce zuwa yanzu an tara naira miliyan ɗaya da dubu ɗari shida.

A cewarsa: "ko wane gari ya biya kuɗin da aka ɗora masa - kuma domin gudun farmaki idan har ba a biya ba, har waɗanda suka gaza biya an ce a ranta don a zauna lafiya."

Ƙauyukan da aka tilastawa mutanensu biyan kuɗin a yankin na Dansadau sun haɗa da Dan Gulbi da Gurmukai da Dambawa da Kundin Kasa da Kundin Sama da Unguwar Zabo da Gudaji wadanda aka tilastawa biyan kudin.

Mazauna ƙauyukan sun ce an tilasta masu biyan ƙudin duk da suna cikin mawuyacin hali na neman abincin da za su ci da kuma kuma cutar kwalara da ta addabe su.

Abin da ya faru

Mutanen Kauyen sun ce ƴan sa-kai ne masu taimakon tsaron ƙauyukan suka kai wa ɓarawon farmaki suka halaka shi a garin ɗan Ma'aji a makon da ya gabata.

Sun ce yana kan babur ya dawo cin kasuwa ya sayar da shanuwa aka kashe shi.

Kuma a cewar Wazirin masarautar Dansadau, mahaifin ɗan fashin da aka kashe ya zo ya ce ya yafe kisan ɗansa amma akwai kuɗi da yake dauke da su da ba a gani ba wanda ya ce dole sai an biya.

Haka kuma sai mutanen ƙauyen sun biya kuɗin babur ɗin ɓarawon da aka ƙone.

Mutanen ƙauyen kuma sun kasa fitar da waɗanda suka aikata kisan, domin gano kuɗaɗen da ake zargin sun salwanta waɗanda yake ɗauke da su bayan kisan shi.

Me uwayen ƙasa suka ce?

Asalin hoton, Other

Wazirin masaraurar Dansadau ya ce ganin halin da suke ciki da kuma yin nisa da gwamnati, uwayen ƙasa suka yanke shawarar cewa ba su da wani zaɓi illa su hada kai a biya kuɗaɗen.

"Wannan ya zama wajibi mu hada karfi da ƙarfi da ƙarfe da talakawa mu biya waɗannan kuɗin," in ji shi.

Ya ce don neman zaman lafiya tare da su aka yi jana'izar gawar mamacin amma a cewarsa bayan jana'izar ne ƴan uwansa suka buƙaci sai an biya su.

Ƙudaden da za su biya sun hada da dubu ɗari biyar na babur da kuma miliyan daya da dubu dari uku da suka ce na dabbar da ya sayar.

A cewarsa "a ranar Juma'a muke fatan za mu kai masu kuɗaɗen kafin cikar wa'adin da suka bayar."

Shugabannin ƙauyukan sun yi kira ga gwamnatin Zamfara ta yi sasanci da ƴan fashin domin su samu kwanciyar hankali

Ya ce akwai ƙauyuka da dama da suka yi sasanci da su kuma suna zaman lafiya har suna zuwa cin kasuwa.

An shafe shekaru 10 ƴan bindiga masu satar mutane da shanu na addabar jihar Zamfara da makwabtanta.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle yayin da yake ganawa da shugabannin ƴan sanda a fadarsa a ranar Laraba ya ce ƴan bindiga sun mamaye wasu ƙauyuka na Zamfara, inda ya nemi a kafa dokar ta-ɓaci a jihohin arewacin Najeriya.

Binciken wata ƙungiya mai zaman kanta ya nuna cewa ƙauyuka kusan 70 ne ƴan bindiga suka mamaye a jihar Zamfara.

Haka kuma ƙungiyar ta ce mutum 364 aka kashe daga watan Fabrairun 2021 zuwa watan Agusta a Zamfara. Ƙungiyar ta kuma ce a shekarar 2021 mutum 1200 aka yi garkuwa da su a jihar kuma kusan mutum 10,000 aka raba da gidajensu.