Afghanistan: Bama-bamai sun tashi a filin jirgin sama na Kabul

Harin bam na Kabul

Asalin hoton, Tolu News Agency

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta tabbatar da mutuwar wasu sojojin kasar a harin bam din da aka kai a filin jirgin saman Kabul, baya ga wasu fararen hula da su ka rasa rayukansu.

Jami'ai sun ce bama-bamai biyu ne su ka fashe -- na farko a bakin kofar shiga filin jirgin mai suna Abbey Gate - wurin da aka ajiye sojojin Amurka da na Birtaniya domin kula da cincirindon dubban masu son ficewa daga kasar -- na biyun kuwa ya tashi ne a otel din Baron da ke kusa.

Wani babban jami'in lafiya ya shaida wa BBC cewa a ƙalla mutum 60 ne suka mutu, 140 kuma suka jikkata a hare-haren.

Daya daga cikin bam din na kunar bakin wake ne, wanda aka tayar sa'o'i bayan da Amurka da kawayenta suka rika yin gargadin aukuwar harin ta'addanci daga kungiyar IS.

Da farko Kungiyar Taliban ta ce mutum 13 ne suka mutu.

Hotunan bidiyo da ake yada wa a shafukan intanet sun nuna gawarwaki masu yawa.

Asibitin da ke bayar da kulawar gagagwa na Kabulya ce an kai kimanin mutum sittin da su ka sami raunuka daga filin jirgin saman.

Jami'an sun ce cikin wadanda suka mutu har da mata da yara sannan wasu dakarun Taliban sun jikkata.

Sannan rahotanni sun ce an yi ta harbe-harbe a wajen.

Bam ɗin ya tashi ne a ƙofar shiga ta Abbey inda dakarun Birtaniya suke a kwanakin nan. Ƙofar na ɗaya daga cikin ƙofofin da aka rufe bayan gargaɗin da aka yi ta yi na barazanar ta'addanci.

Wani jami'in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya tayar da bam ɗin.

Fadar White House ta tabbatar da cewa an shaida wa Shugaba Biden halin da ake ciki.

Ita ma Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta ce bama-bamai biyu ne suka tashi a wajen filin jirgin sama na Kabul. Babu tabbas kan hakan.

Dama jami'an ƙasashen yamma sun umarci dandazon mutanen da suka taru a ƙofofin shiga filin jirgin da su bar wajen saboda ana zaton za a iya kai harin ta'addanci.

Kazalika ba a samu hotuna sosai ba na abin da ke faruwa a filin jirgin a ranar Alhamis, don haka ba a sani ba ko mutane sun ji gargaɗin sun kuma bi umarnin.

Kafar yaɗa labaran Tolo ta Afghanistan ta ce an tafi da mutane da dama sun jikkata a tashin bam ɗin zuwa asibiti.

Fargabar sake tashin wani bam ɗin

Bayanan hoto,

Mutum 60 ne suka mytu ciki har da mata da yara

Jakadan Faransa da ke Kabul, David Martinon, ya roƙi mutane da su bar wajen ƙofofin shiga filin jirgin sama saboda fargabar sake tashin wani bam ɗin.

Ya wallafa a Tuwita cewa: "Ga dukkan abokanmu na Afghanistan, idan har kuna kusa da ƙofofin shiga filin jirgin sama to kua bar wajen da gaggawa ku nemi mafaka - akwai yiwuwar sake tashin wani bam ɗin."

Jakadan na Faransa ya yi jimamin mutuwar wadanda suka rasu amma ya ce lamarin bai shafi ɗan Faransa ko ɗaya ba.

"Babu wani soja ko ɗan sandan Faransa ko jami'in diflomasiyya da yake bakin ƙofar Abbey inda abin ya faru.

Abin da ya faru

Ainihin abin da ya faru shi ne tashin bam sau ɗaya amma ba da jimawa ba sai wani ya sake tashi da kuma harbe-harbe, a cewar wakilin BBC Jonathan Beale.

Dukkan bama-baman sun tashi ne a kusa da ƙofar shiga filin jirgin sama ta Abbey inda ƴan gudun hijirar Afghanistan da dama suka yi cincirindo tsawon kwanaki.

Hotuna sun yaɗu na halin da ake ciki bayan tashin bam ɗin, inda aka ga mutanen da suka ji rauni kaca-kaca cikin jini ana ɗaukar su a wulbaro.

Kafar yaɗa labaran Afghanistan ta Tolu ta wallafa hotunan a Tuwita da ke nuna maza da yara - wasu ɗaure da bandeji a kawunansu - suna ta tserewa daga wajen.

Akwai hotunan da ka iya ɗaga muku hankali

Wani ɗan jarida Bilal Sarwary - wanda ya bar ƙasar kwanaki kaɗan da suka wuce - ya ce ya yi magana da wani abokinsa da ke kan layi a filin jirgin saman minti 15 kafin bam ɗin ya tashi.

Ya ce abokin nasa ya ga yadda ake ɗaukar waɗanda suka jikkata. "Hakan na nufin motar ɗaukar marasa lafiya ba za ta iya shiga wajen ba," in ji shi.

Amurkawa nawa ne uka mutu?

Jami'ai sun shaida kafafen yada labaran Amurka cewa dakarun kasar 12 ne suka mutu a harin.

Mace-macen su ne na farko na sojojin Amurka a Afghanistan tun watan Fabrairun 2020.

Tashin bam kusa da otel

Alicia Kearns, wata mamba na kwamitocin harkokin ƙasashen waje da tsaron cikin gida, ta ce mutane da dama sun jikkara a wani hari kusa da otel ɗin NBaron, inda Birtaniya ke aikin tantance ƴan ƙasarta da ƴan Afghanistan da take son kwashewa.

Ƴar majalisar dokokin ta wallafa a Tuwita cewa: "Wani bam ya tashi ko kuma an kai wani hari a ƙofar shiga Baron Hotel daga arewa. Hakan zai dagula lamarin kwashe mutane da ake yi - akwai takaici sosai. Ina jimamin mutuwar waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka jikkata.

Wa ya kai harin?

Sa'o;i bayan kai harin dai Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren bam da aka kai filin jirgin sama na Kabul.

Ikirarin ya biyo bayan wani sako ne da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Kungiyar ta ce wani dan kunar bakin wake ne - ya sanya rigar bam ya shiga tsakanin 'yan Afghanistan da dakarun Amurka.

Jami'an hukumar tsaron Amurka sun ce sun yi amannar mayakan IS da ke yankin ne suka kai harin.