Wane ne ya lashe gasar labarin manahajar podcast na kasa da kasa na BBC na farko?

Podcast BBC

Wata 'yar kasar Kenya Namulanta Kombo mai shekara 38 ce ta lashe Gasar yada shirye-shirye ta manahajar Podcast ta kasa da kasa ta farko da kafar yada labarai ta BBC ta shirya.

A gasar wacce aka kaddamar a cikin wannan shekarar, an bayar da dama ga wadanda ba ma'aikatan kafofin yada labarai ta rediyo da talabijin ko manahajar podcast ba ne daga kasashen Kenya, da Najeriya da Afirka Ta Kudu.

An kuma samu gagarumar nasara, da kusan mutum 1,000 da suka shiga gasar.

Yanzu haka BBC za ta taimaka wa Namulanta, wacce ba ta taɓa amfani da manahajar ta podcast ba, wajen fito da labarin nata mai taken ''To My Daughter'' wato ''Zuwa ga 'Yata'' mai bangarori 15 da ya lashe gasar, da nan gaba cikin wannan shekar za a kaddamar.

Lakabin labarin podcast din ya fito da irin shawarar da Namulanta ta yanke na fara rubuta wasiku ga karamar 'yarta.

A labarin za kuma a ji abubuwan da suka faru, da labarai da shawarwari daga iyaye a fadin kasashen Afirka, da kuma fadin duniya da suke so su bayyana wa 'ya'yansu mata.

Yayin da take magana game da lashe gasar, Namulanta ta ce: "Fuskantar yawan shekaru da kallon kaina a matsayin 'yata, na damu game da abin da zai faru idan aka ce ba na kusa da zan iya taimaka mata fuskantar rayuwa, ko kuma idan ina nan din amma ta ji cewa ba za ta iya yi min magana ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Na fara tunanin wata shawara ta rubuta wani ''dan littafin rayuwa'' da zai hada kananan labarai daga mutanen da ke kewaye da mu wuri guda."

"Na nemi abokai da iyalai su rubuta wasiku zuwa ga matan da suke cikin rayuwarsu, kana na yi la'akari da hanya mafi kyau da zan fitar da wadannan wasiku ga duniya.

"BBC ta bullo da gasa kuma na ga cewa na samu wata dama da zan hada wadannan tunane-tunene nawa wuri guda in tsara shawarata.''

Gasar na neman ingantacciyar basira ta labarin manahajar podcast.

Darakta Janar na BBC Tim Davie ya bayyana cewa: "BBC na neman shawarwari na podcast masu ma'ana da za su zaburar da mata a fadin duniya.

"Mun kuma ji dadin samun tarin masu gasar masu shiga gasar masu inganci.

"Daya daga cikin shawarwarin ta yi fice. Labarin podcast na Namulanta Kombo zai mika sakon wasiku daga mata a fadin duniya zuwa ga 'yayansu mata.

Shawara ce ma matukar amfani da kuma wacce za ta kawo cigaba. Na kagara in fara jin kashi na farko."

Wace ce Namulanta?

An haifi Namulanta a Nairobi babban birnin kasar Kenya, kuma ta shafe shekaru tara tana aiki a bangaren cigaban al'amura a kan ayyukan da suka shafi 'yan kasar Kenya tare da tallafa wa hukumomin gwamnati wajen sa ido, da tantancewa da kuma ayyuka kan manufofin gwamnati.

Tana kuma aiki kai tsaye tare da kananan yara, tana kula da wuraren shakatawa da wasanni don bunkasa ilimi ta hanyar wasanni da kuma tsara gasar fasashohi da kuma ranakun shakatawar iyalai.

Alkalai sun yi nuni da tarin gasar da suka shigo daga jama'a, wadanda aka tankade da rairaye sun hada daga duka kasashe uku da suka cancanci shiga gasar.

Alkalan da zagayen karshe na gasar sun hada da:

  • Kenya - Paula Rogo wanda ya kirkiri kafar yada labarai ta Kali Media kana daya daga cikin wadanda suka kirkiri Africa Podfest'
  • Afirka Ta Kudu- Jedi Ramalapa na Sound Africa
  • Nigeria - FayFay (Odudu Efe), wanda ya koya wa mutane 1,500 aiki da manahajar podcast a Najeriya ta hanyar bude cibiyar Naija Pod Hub
  • Jon Manel, Editan raba aikin podcast BBC World Service (shugaba)
  • Mary Hockaday, kwantrolan sashen Turanci na BBC World Service
  • Jonny Kanagasooriam, Babban Manajan Tsare-tsare, BBC Sounds
  • Sharon Machira, mai gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin na BBC a kasar Kenya.

Paula Rogo ta ce gasar da ta samu galaba: '' shawara ce mai sauki tare da jan hankalin duniya. Wata aba ce da ba matan Afirka kadai ba, har ma da mata a kasashen duniua za su amfana da shi.

"Na yaba da irin wannan basira da nag ani. Akwai wasu shawarwari da idan aka sakar musu kudaden da suak dace da kuma goyon baya, za su yi matukar kyau da zarar an fara amfani da su."

Ana sa ran kaddamar da labarin podcast na Namulanta a watan Disambar shekarar 2021.

Za a sake gudanar da gasar a farkon shekarar 2022 - nan gaba kadan za a sanar da kasashen da za su shiga.