Manchester City ta sayi Ronaldo, Aubameyang ba zai bar Arsenal ba

Cristiano Ronaldo ya koma Juventus a 2018 a kan kusan yuro miliyan 112

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cristiano Ronaldo ya koma Juventus a 2018 a kan kusan yuro miliyan 112

Ciniki ya fada tsakanin Manchester City da Juventus a kan Cristiano Ronaldo, kyaftin din Portugal mai shekara 36. (Jaridar AS)

Juventus ta bukaci tsakanin yuro miliyan 25 zuwa 30 (fam miliyan 21-25) a kan Ronaldo, inda ake sa ran City za ta ba shi kwantiragin shekara biyu. (Jaridar Guardian)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pep Guardiola na kociyan Barcelona lokacin da Cristiano Ronaldo yake Real Madrid

Kungiyar ta Italiya ta so Ronaldo ya tsaya, amma kuma rashin yardarsa ya sa take son maye gurbinsa da dan gaban Man City din kuma dan Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 24. (Sky Sports)

Asalin hoton, Getty Images

Wolverhampton Wanderers ta yi watsi da bukatar Tottenham Hotspur, ta bayar da aron dan wasanta na gaba na gefe, Adama Traore mai shekara 25, saboda tana son ci gaba da zama da dan Sifaniyar. (Telegraph)

West Ham United na harin dan gaban CSKA Moscow dan Croatia Nikola Vlasic, mai shekara 23, a kokarin da kungiyar take yi na neman wanda zai maye gurbin Jesse Lingard na Manchester United da ta karba aro. (Sky Sports)

Watford ta fara tattaunawa da Tottenham domin sayen dan wasan tsakiya na Faransa Moussa Sissoko, mai shekara 32. (Fabrizio Romano)

Paris St-Germain na kokarin sayo wasu 'yan wasa da suka hada da Paul Pogba, na Manchester United da Faransa da Erling Braut Haaland, na Borussia Dortmund dan Norway mai shekara 21, yayin da kungiyar ta Faransa ke shirya wa kakar da za su yi ba tare da Kylian Mbappe ba. (L'Equipe)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana danganta Erling Braut Haaland da tafiya Manchester City

Real Madrid ta kara kudi a tayin da ta yi na Mbappe yanzu zuwa fam miliyan 145 bayan da PSG ta ki sallama matashin a tayin da ta fara yi na fam miliyan 137. (Sky Sports)

Manchester United ta kuskure samun matashin dan wasan gaba na gefe na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, Noni Madueke, mai shekara 19, bayan da ya sanya hannu a sabon kwantiragi da PSV Eindhoven. (Jaridar Mirror)

Harry Kane na tattaunawa a kan sabon kwantiragi da kungiyar tasa Tottenham. Dan gaban mai shekara 28, na fatan kulla yarjejeniyar da zai rika karbar albashin fam dubu 400 a mako, bayan da ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar ta London a bana.(Times)

Chelsea na daf da kammala daukar dan bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 22, a cinikin da ya kai na fam miliyan 42. (Sky Italia, ta jaridar Star)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Da farko Sevilla ta ki yarda da tayin da Chelsea ta yi a kan Jules Kounde amma yanzu cinikin na dab da tabbata

Shi kuwa dan bayan Chelsea Kurt Zouma, mai shekara 26, zai je a duba lafiyarsa kafin ya kammala tafiya West Ham da ta saye shi fam miliyan 26 a yarjejeniyar shekara biyar. (Jaridar Sun)

Tottenham ta fara tattaunawa domin sayen dan wasan tsakiya na Juventus, Ba'amurke Weston McKennie, mai shekara 22 a kan fam miliyan 40. (Jaridar Independent)

Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya kawar da yuwuwar tafiyar kyaftin din kungiyar dan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang daga kungiyar. (ESPN)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daman Arteta ya ce yana da kwarin guiwa Aubameyang wanda ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a Janairun 2018, ba zai tafi ba

Everton na sha'awar sayen dan gaban Brighton, dan Farnsa Neal Maupay mai shekara 25. (Sky Sports)

Manchester United za ta nemi sayen wani dan wasan tsakiya kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa da ke ci a yanzu, amma kuma kila sai ta jira a kan dan Ingila Declan Rice na West Ham mai shekara 22. (Jaridar Independent)