Afghanistan: Amurka ta lashi takobin hukunta maharan Kabul

Joe Biden ya ce hare-haren ba za su hana su aiwatar da ayyukansu a Afghanistan ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Biden ya ce hare-haren ba za su ba su tsoro ba

Shugaban Amurka Joe Biden ya lashi takobin farauto wadanda suka kai tagwayen hare-haren Kabul babban birnin Afghanistan, ranar Alhamis, da suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 60 da raunata wasu 140, yana cewa za su dandana kudarsu.

Ya kuma ce za a ci gaba da aikin kwashe mutanen da ake yi a kuma kamala shi, duk da barazanar maharan.

Zuwa yanzu dai an kwashe sama da mutane dubu 100 daga birnin na Kabul wanda ya fada hannun 'yan Taliban ranar 15 ga watan nan na Agusta.

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Biden ya ce ko kadan wadannan hare-hare biyu da suka hallaka mutane kusan da 90, da suka hada da sojojin Amurka 13, ba za su hana su wannan aiki ba.

Ya ce dole ne za su kammala aikin kwashe mutanen kuma lalle za su yi. Sannan ya sha alwashin farauto wadanda suke da alhakin kai hare-haren domin su girbi abin da suka shuka.

Zuwa yanzu dai an kwashe sama da mutane dubu 100 daga birnin na Kabul wanda ya fada hannun 'yan Taliban ranar 15 ga watan nan na Agusta.

Amma kuma akwai da dama 'yan kasar ta Afghanistan da ke tururuwa zuwa filin jirgin sama na Kabul, domin a fitar da su daga kasar kafin wa'adin ranar 31 ga wata na Agustan, na ficewar sojojin Amurka daga kasar.

Harin da aka kai ranar Alhamis na farko ya auku ne a wata kofa; Abbey Gate inda sojojin Amurka da na Burtaniya ke tantance mutanen da ke shiga filin jirgin saman, bayan tashin bam ne sai kuma aka bude wuta.

'Yan mintuna kadan tsakani kuma sai bam na biyu ya tashi a wani otal, wanda jami'an Burtaniya ke amfani da shi domin tantance 'yan Afghanistan da ke son ficewa zuwa Burtaniyar.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tarin mutane ne dama ne suka yi cuncurundo a wuraren da aka kai harin, da ke fatan a bar su su shiga jirgin saman da ke kwashe jama'a, duk da gargadin da Amurka da Burtaniya suka yi na hadarin fuskantar harin kunar bakin-wake daga wata kungiya mai alaka da ISIS, wadda Shugaba Biden ya mata lakabi da Isis-K.

Kungiyar ta masu ikirarin jihadi daga bisani ta fitar da sanarwar daukar alhakin hare-haren na Alhamis.

Mutuwar ita ce ta farko ga sojojin Amurka a Afghanistan tun watan Fabrairu na shekarar da ta gabata, 2020.

Shugaba Biden ya jinjina wa dakarun da suka mutu, wadanda ya bayyana da cewa gwaraza ne da ke kan aikin sadaukar da kai don ceto rayuwar wasu.

Babban hafsan da ke jagorantar dakarun Amurkar a kasar, Janar Frank McKenzie ya ce har yanzu akwai barazana sosai ta hare-hare daga kungiyar ta Isis-K.

Kuma sojojin Amurka suna aiki tare da 'yan Taliban domin hana kai karin hare-hare, wanda daman Taliban din ta kare da dama in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana iya ganin yadda hayaki ya turnuke birnin bayan tashin bama-baman

Sai dai ana ganin kila harin na Alhamis ya dan rikita aikin kwashe mutanen kafin wa'adin da aka diba.

A yanzu dai akwai sojojin Amurka 5,800 a filin jirgin sama na Kabul, da kuma karin wasu na Burtaniya 1,000.

Zuwa lokacin wannan rahoto an kwashe farar hula 104,000 daga Afghanistan, da suka hada da dubu 66 'yan Amurka da dubu 37 daga kasashen kawance.

Akwai mutane wurin 5000 a filin jirgin saman na Kabul da ke jiran a kwashe su, da kuma wasu dubban da ke neman shiga harabar filin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dubban mutane na jiran a kwashe su a filin jirgin Kabul

Kasashe da dama da suka hada da Canada da Belgium da Holland da Denmark sun dakatar da aikin kwasar mutane.

Turkiyya kuma wadda sojojinta suka yi shekara shida suna samar da tsaro a filin jirgin ta ce za ta janye

Firaministan Burtaniya Boris Johnson, wanda ya jagoranci wani taron manyan jami'ai kan halin da ake ciki a Afghanistan ya ce jiragen kasarsa na kwashe mutanen za su ci gaba da aiki.

Shugabannin kasashen Yammacin Duniya na ci gaba da suka da tir kan hare-haren na Kabul.