Harin filin jirgin saman Kabul: Me muka sani game da shi?

  • Daga The Visual Journalism Team
  • BBC News
...

Asalin hoton, Getty Images

Manyan bama-bamai biyu dai sun tashi a katangar filin jirgin saman kasa da kasa na Hamid Karzai da ke Kabul, a yayin da 'yan kasar suke ci gaba da neman tserewa daga kasar Afghanistan wadda 'yan Taliban suka kwace ikonta.

Akalla mutum 90 aka kashe sannan mutum 150 suka jikkata, a cewar wani babban jami'in lafiya a Kabul a hirarsa da BBC.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da mutuwar dakarun Amurka 13.

Bama-baman sun tashi ne sa'o'i kadan bayan gwamnatocin Kasashen Yammacin Duniya sun gargadi mutanensu da su guji zuwa filin jirgin saman, saboda yiwuwar kai hare-haren kungiyar IS-K, wani reshen kungiyar Islamic State da ke Afghanistan.

Ga abubuwan da muka sani game da tashin bama-baman kawo yanzu

Bama-baman sun tashi ne a wajen filin jirgin saman

Bam na farko ya tashi ne da misalin karfe 6 na yamma a agogon Kabul (13:30 GMT), kusa da otal mai suna Baron, da ke dab da katangar filin jirgin saman.

Jami'an Birtaniya wadanda suke tantance 'yan kasar Afghnaistan da ke fatan tafiya Birtaniyar ne suke zama a otal din.

Daga baya an bude wuta da bindigogi sannan sai bam na biyu ya fashe a kusa da Kofar Abbey, daya daga cikin kofofin shiga filin jirgin saman.

Rahotanni sun ce bam na biyu ya tashi ne kusa da wata kwata inda 'yan kasar Afghnistan suke jira a tantance su, kusa da kofar shiga, kuma wasu daga cikinsu sun fada kwata.

Wani jami'in Amurka ya ce akalla daya daga cikin maharan yana sanye da rigar bam.

Kwanakin baya an tura dakarun Amurka da na Birtaniya domin su yi gadin yankin da ke kusa da Kofar Abbey.

A cewar wata majiya, daya daga cikin maharan ya bude wuta kan dandazon jama'a, ko da yake wasu rahotanni sun ce masu gadi daga bangaren Taliban sun yi harbi a sama.

'Yan kasar Amurka da suka je yankunan da ke kusa da filin jirgin kafin faruwar lamarin an gargade su da su bar wurin "nan take".

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Birtaniya sun soma gadin katangar da ke kewayen Otal din Baron bayan tashin bama-baman

Mutanen da suka mutu

Alkaluman mutanen da suka mutu suna ci gaba da karuwa.

Babu wata tabbatacciyar kididdiga a baya bayan nan game da Amurkawa da 'yan kasar Afghanistan - ciki har da 'yan Taliban - da suka mutu.

Sai dai ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce dakarun Amurka 13 ne suka mutu sannan 15 sun jikkata. Wani babban jami'in lafiya na Birtaniya a Kabul ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 90 sun mutu, sannan mutum 150 suka jikkata.

Hotunan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ake daukar wadanda suka jikkata a wul baro.

Dandazon jama'a ne ya rika taruwa a yankin, inda suke fatan za a dauke su a jirage zuwa kasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana iya ganin hayaki yana tashi sama bayan tashin bama-baman

Wasu kasashe sun dakatar da kwashe 'ya'yansu

Mai yiwuwa harin zai yi tasiri kan yunkurin da ake yi na kwashe dubban mutane daga Afghanistan.

Kafin kai harin, wasu kasashe cikinsu har da Jamus, Netherlands da Canada, sun bayyana cewa ba za su ci gaba da kwashe mutane ba.

Turkiyya ta sanar cewa dakarunta, wadanda suka kwashe shekara shida suna samar da tsaro, za ta janye su.

Hotuna daga Prina Shah and Gerry Fletcher