Shin shan ruwan sanyi na da amfani a jikin dan adam? Ga abubuwan da ilimin kimiyya ke fada a kai

cold water

Asalin hoton, Corina Pop / EyeEm

Mutane da na ra'ayoyi daban-daban game da shan ruwan kankara.

Wasu sun yi amanna cewa shan ruwan sanyi yana yin mummunan tasiri kan yanayin narkewar abinci a jikin dan adam kana yana haifar da dankarewar majina.

Wasu kuma na cewa ruwan sanyin na sa mutane su kona kitse lokacin da jiki ke sarrafa abincin da suka ci kana yana taimakawa yayin motsa jiki.

Shin menene gaskiya?

Shin yana da kyau mutum ya sha kofi daya na ruwan kankara a lokacin da ake fama da zafi mai tsanani?

Takaitaccen bayani shi ne—Ee, haka ne.

Babu wadatattun shaidun kimiyya da ke ikirarin cewa shan ruwa mai tsananin sanyi ba shi da kyau ga jikin dan adam.

Kana wani babban tasirin shan ruwan kankara — don kashe kishin-ruwa.

Dalilan da suka sanya shan ruwa mai tsananin sanyi zai taimaka wajen kashe kishin-ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Da farko, yana da matukar muhimmanci a san cewa shan ruwa a ko wane irin yanayi zai taimaka wajen mayar da ruwan jiki.

Yana da matukar muhimmanci mutum kullum ya kasance yana da isasshen ruwa a jiki don taimakawa wajen daidata yanayin zafin jikin.

Ruwan jikin kan taimaka wa kayan cikin mutum gudanar da aiki sosai, samar da abubuwa masu gina jiki ga kwayoyin halitta.

Kana yana kuma taimakawa wajen bayar da kariya daga kamuwa da cututtuka kamar yadda cibiyar kula da lafiya Harvard Health ta bayyana.

Shin shan ruwan sanyi na da kyau a jiki?Karanta abinda ilimin kimiyya ya fada a kai

Shan ruwa a ko wane irin yanayii- sanyi ko zafi ko kuma dun ikan taimaka da mayar da ruwan jiki.

Amma kuma, an tabbatar da cewa shan ruwan sanyi na taimakawa wajen mayar da ruwan jiki fiye da ruwan dumi ko kuma wanda marar sanyi ko zafin.

Akwai wani bincike da mujallar kiwon lafiya ta International Journal of Clinical and Experimental Medicine ta gudanar a kan wasu maza 'yan wasan motsa jiki shida game da wannan.

Dukkanninsu sun sha ruwa masu yanayi daban-daban.

An gano cewa shan ruwa mai yanayin ma'aunin zafi 16 (16 degrees Celsius) ko kuma (~60 degrees Fahrenheit) da kuma shan ruwa mafi yawa ya haifar da zufa kadan.

Hakan ya nuna cewa ya fi idan aka kwatanta da sauran.

Wani bincike daga mujallar Human Kinetics Journal ya gano cewa wanka da ruwan sanyi daga famfon shaya an minti 10 bayan motsa jiki na minti 20 zai taimaka wajen kara ruwan jiki.

Idan aka hada da minti 10 na wankan ( wanda aka fi sani da ''gwajin ruwan sany'') ya tabbatar da taimakawa wajen warkewar tsokar jiki ga masu wasan motsa jiki.

Da amfani mai yawa da shan ruwan sanyi ke da shi, wasu kwararru kan kiwon lafiya sun ce;

Shan ruwa sanyi ba shi da kyau ga jikin dan adam amma mutane da dama sun tabbatar da cewa a na su ganin hakan ba gaskiya bane.Binciken ya karkare da cewa ruwan famfo mai sanyi ya fi zama mafi kyau wajen samu yanayin zafin jikin da sahn ruwan kan haifar, musamman wanda ke aiki a cikin yanayin zafi mai tsanani.

Shaci-fadi a kan shan ruwan sanyi

Asalin hoton, Getty Images

Masu ilimin magungunan gargajiya na kasar India sun bayyana cewa shan ruwan kankara ba shi da kyau wajen narkewar abinci a jikin dan adam.

Sun yi ikirarin cewa ruwan sanyi kan iya tsuke jijioyin jini, wadanda ke sarrafa wasu sinadaran gina jiki kamar - vitamins, da kuma abinci.

Shan ruwan dumi al'ada ce ga mutane da dama, da suka yi amanna cewa ruwan dumin na taimakawa wajen narkewar abinci cikin sauri.

Hada da kuma cewa yana da kyau wajen lafiyar cikin mutum.

Binciken ya duba yadda sanyi ke shafar jikin hanyoyin jinni da kuma yanayin zafin jikin karnuka.

A yayin da gaskiya ne cewa lokacin sanyi na shafat yanayin zagayawar jinin jiki, wannan bincike bai mayar da hankali kan yadda shan ruwan kankara ke shafar hanyoyin jini kai tsaye ba.

Gaba daya, yayin da hanyoyin jinin ke taka muhimmiyar rawa wajen narkewar abinci, babu wasu gamsassun shaidu na kimiyya da ke nuna sahihancin ikirarin da suka yi;

Shan ruwan sanyi ka iya haifar da jinkiri wajen narkewar abinci.

Akwai sauran rashin fahimta game da shan ruwan kankararna haifar da taruwar majina.

Wannan na zuwa ne daga wani bincike na shekarar 1978 daga mujallar CHEST wacce ta auna majinar kafofin hanci da karfin iskar shaka.

Amma kuma, yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa an adana wannan bincike a dakin ajiyar litattafan kiwon lafiya ta Amurka.

Amma kuma, binciken na nan a shafin intanet na mujallar ta CHEST don sake yi masa garanbawul.

Daga karfe kuma, daya ikirarin ya nuna cewa shan ruwan sanyi zai iya saka ka jin tsananin yunwa.

An fara wannan ikirari ne a cikin binciken shekarar 2005 daga Jami'ar Florida.

An kuma kwatanta binciken tsakanin mutanen da suka ci abinci da kuma wadanda ke motsa jiki ta hanyar amfani da ruwan sanyi da na dumi.

Kuma ya karkare da cewa wadanda ke hada motsa jiki da shan ruwan sanyi za su iya ''samun kuzari sosai saboda motsa jikin''.

Hakan ka iya saka su jin matsananciyar yunwa da kuma cin abinci sosai.

Sauran binciken sun nuna cewa mutane na jin yunwa sosai a lokacin sanyi fiye da sauran lokutan.

Amma kuma, hakan bai karkare cewa shan ruwan sanyi ka iya haifar da karin lafiya ba.