Hare-haren September 11: Abin da ya faru ranar da bayan hare-haren
- Daga Patrick Jackson
- BBC News

Asalin hoton, Getty Images
Ran 11 ga watan Satumban 2001 wasu ƴan ƙunar baƙin wake suka ƙwace iko da jiragen dakon fasinjojin Amurka kuma suka faɗa wasu dogayen gine-gine biyu a birnin New York kuma suka kashe dubban mutane.
Harin ya kasance ɗaya daga cikin hare-hare mafiya muni a wannan ƙarnin, ba ga Amurkawa ba kawai ga duniya baki ɗaya.
Wa aka so a kai wa hari?
Wasu ƙananan tawagogin mahara sun ƙwace iko da jirage huɗu da ke tafiya a sararin samaniyar gabashin Amurka.
Daga nan sai suka ja ragamar tuƙin jiragen suka auka manyan gine-gine a New York da Washington.
Jirage biyu sun faɗa cikin tagwayen ginin Twin Towers na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya wato World Trade Centre a New York.
Jirgin farko a ya fada North Tower wadda da ƙarfe 8:46 ko ƙarfe 13:46 agogon GMT. Na biyun kuma ya fada ɗaya ginin da ƙarfe 09:03.
Gine-ginen sun kama da wuta kuma mutane sun maƙale a ciki inda hayaƙi ya turniƙe gaba ɗaya birnin. Cikin ƙasa da sa'a biyu, tagwayen gine-ginen masu hawa 110 suka rushe.
Da ƙarfe 09:37 jirgi na uku ya auka sashen yamma na ginin Pentagon - babbar hedikwatar ma'aikatar tsaron Amurka da ke wajen Washington DC, babban birnin Amurka.
Jirgi na huɗu ya faɗi a wani fili a Pennsylvania da ƙarfe 10:03 bayan da fasinjojin suka ƙalubalanci maharan. Ana tunanin maharan sun yi ƙoƙarin kai hari ne kan ginin majalisar dokoki na Capito; Building da ke Washington DC.
Asalin hoton, Getty Images
Wasu mazauna New York suna gujewa hayaƙi dalilin harin
Mutane nawa ne suka mutu?
Gaba ɗaya, mutum 2,977 (ban da maharan 19) suka rasa rayukansu mafi yawansu a birnin New York.
- Duka fasinjojin 246 da ma'aikatan jiragen hudu sun rasu
- A tagwayen gine-ginen mutum 2,606 sun rasu - a take ko daga baya sanadin raunukansu
- A Pentagon, mutum 125 ne suka rasu
Mafi ƙarancin shekaru cikin waɗanda suka mutu wata jaririya ce mai shekara biyu Christine lee Hanson wadda ta rasu tare da iyayenta Peter da Sue a daya daga cikin jiragen.
Mafi yawan shekaru kuwa Robert Norton mai shekaru 82 wanda ya ke wani daga cikin jiragen tare da matarsa Jacqueline a hanyarsu ta zuwa wani bikin aure.
Lokacin da jirgin farko ya faɗi, an yi ƙiyasin mutum 17,400 suna cikin tagwayen ginin. Babu wanda ya tsira a ɓangaren arewa ko North Tower ta inda nan ne jirgin ya fara kutsa kai, amma mutum 18 sun yi tsere daga hawan da ke saman inda jirgin ya shiga a ɓangaren kudanci wato South Tower.
Mutane ƴan asalin ƙasashe 77 na cikin wadanda harin ya rutsa da su. Birnin New York ya rasa ma'aikatan agaji 441.
Dubban mutane sun samu raunuka yayin da wasu suka gamu da wasu cutukan sanadiyyar hare-haren, ciki har da ƴan kwana-kwana da suka shaƙi guba a gine-ginen da suka rushe.
Asalin hoton, Getty Images
Su waye maharan?
Wata ƙungiya mai tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci mai suna al-Qaeda ce ta shirya harin daga Afghanistan.
Ƙarƙashin jagorancin Osama Bin Laden, al-Qaeda ta zargi Amurka da ƙawayenta da janyo rikici a kasashen Musulmi.
Mutum goma sha tara ne suka kai harin, inda suka kasa kansu cikin tawagogi uku masu ɗauke da mutum biyar-biyar da guda daya mai ɗauke da mutu huɗu (a jirgin da ya faɗi a Pennsylvania).
Ko wace tawaga na ɗauke da mutum ɗaya da aka yi wa horon tuƙin jirgi. Sun yi horon ne a makarantun koyon tuƙin jirgi a Amurka.
Goma sha biyar daga cikin maharan ƴan Saudiyya ne, kamar Bin Laden. Biyu ƴan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne, ɗaya ɗan masar ne sannan daya ɗan Lebanon ne.
Ya Amurka ta mayar da martani?
Ƙasa da wata ɗaya bayan kai hare-haren, Shugaba George W Bush ya jagoranci tura dakaru Afghanistan - tare da goyon bayan wata haɗin guiwar kasashen waje - don kawo ƙarshen al-Qaeda da kuma kamo Bin Laden.
Sai dai ba a kama Bin Laden ba sa shekarar 2011 inda sojojin Amurka suna kashe shi a Pakistan.
Amurka ta kama wanda ake zargi da shirya hare-haren 9/11, Khalid Sheikh Mohammad, a Pakistan a 2003. Kawo yanzu yana nan a tsare a gidan yarin Guantanamo Bay yana jiran shari'a.
Kuma kawo yanzu al-Qaeda na nan. Ta fi ƙarfi a yankin kudu da hamadar sahara amma har yanzu tana da mabobi a Afghanistan.
Dakarun Amurka sun fice daga Afghanistan a wannan shekarar bayan kusan shekaru 20, kuma wannan ya jefa mutane da dama cikin fargabar cewa ƙungiyar na iya sake fito da ƙumbarta.
Asalin hoton, Getty Images
Tarin hotunan mutanen da suka rasa rayukansu ran 11 ga Satumba, 2001 a wani gidan ajiye tarihi a New York
Abin da hare-haren 9/11 suka bari
An ƙarfafa matakan tsaro a filayen jirgin sama a fadin duniya bayan aukuwar hare-haren 9/11.
A Amurka, an kafa Hukumar Kula da Tsaron Sufuri don ƙara ƙarfin tsaro a filayen jirgi da a kan jiragen.
An ɗauki kusan wata takwas kafin a kammala kwashe ɓaraguzan tagwayen ginin.
Da aka kammala kwashewa, an gina wani gidan ajiye kayan tarihi da wani tambarin tunanwa da waɗanda suka rasu a madadin gine-ginen, an kuma yi wasu manyan gine-gine da wani fasali na daban.
Daga tsakiya an gina - One World Trade Center ko "Freedom Tower" - wanda tsawonsa ya fi yadda yake a da.
An gyara ginin Pentagon cikin ƙasa da shekara ɗaya, kuma ma'aikata sun koma ofisoshinsu cikin watan Agustan 2002.