Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 29 ga Agusta zuwa Asabar 04 ga Satumba.

Sauke ministocin Buhari biyu

Bayanan hoto,

Ministocin da Shugaba Buhari ya sauke na Ma'aikatun Lantarki da kuma na Noma

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma'aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a ranar Larabar bayan taron majalisar koli.

Mista Adesina ya ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayin da karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.

Matakin wani ɓangare ne na sauye-sauyen da shugaba Buhari ke aiwatarwa, a cewar Femi Adesina.

A shekara ta 2019 Buhari ya fitar da sunayen mutanen biyu cikin waɗanda yake son naɗawa a matsayin ministoci, kuma majalisa bayan tantacewa ta amince da naɗin nasu.

A baya dai Ministan Noma Sabo Nanono ya sha janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'umma musamman lokacin da ya yi batun cewa naira 30 za ta ishi mutum ya ci abinci a Kano.

An sake satar ɗalibai da dama a Zamfara

A ranar Laraba ne ƴan bindiga suka kai hari wata makarantar sakandare a karamar hukumar Maradun inda suka sace dalibai da dama.

Hukumomi a Zamfara sun ce ɗalibai 73 ɓarayin suka sace a harin makarantar ta jeka ka dawo ta Kaya.

Rahotanni sun ce dalibai fiye da 400 ne suke makarantar lokacin da aka kai harin suna masu karawa da cewa daliban suna rubuta jarrabawar 'Mock' ta 'yan aji biyar ne lokacin da aka kai harin.

A cewarsa, daga nan ne suka watse suka shiga cikin gonar gero tare da wasu daliban amma duk da haka 'yan bindigar sun kwashe dalibai da dama.

Wannan na faruwa ne, bayan sako ɗaliban kwalejin noma da lafiyar dabbobi ta Bakura.

Sabbin matakan tsaro a jihohin arewa maso yammaci

Asalin hoton, NDHQ

Gwamnatocin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun ɗauki wasu sabbin matakai na kawo karshen hare-haren 'yan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa.

Matakan sun hada da hana bude kasuwannin da ke ci mako-mako da takaita yawan man fetur din da za a sayar da sauransu.

Jihohin da suka ɗauki wannan mataki sun hada da Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja da Sokoto.

An kuma hana fitar dare da rufe makarantu a jihar Zamfara.

Jihohin sun ce matakan na da nasaba da kokarin ganin sun toshewa 'yan bindigar duk wata kofa ta sararawa ko ta samun kayan da suke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare.

Mutum 784,000 ke gudun hijira a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Kwamishinar da ke lura da ayyukan jinkai da agajin gaggawa ta jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Hajiya Fa'ika Ahmad, ta ce suna ta fama da 'yan cirani a jihar da sukai 784,000.

Kwamishinar ta ce cikin adadin akwai sama da 184,000 da mata ne sai kuma kananan yara da suka kai 600,000.

Hajiya Fa'ika ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da take karbar kayan abinci da kuma wasu sauran kayan jinkai da ma'aikatar agaji ta kasa ta bayar.

Mataimaki na musamman ga Minista Sadiya Faruk, Alhaji Musa Ahmad Bungudu ne ya mika kayan ga hukumomin jihar.

Kwamishinar ta ce akwai tashin hankali idan aka kalli adadin mata da yaran da suka samu kansu cikin wannan yanayi, dan haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da Najeriya ta karbi 'yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.

Jamb ta soke ƙayyade wa Jami'o'i makin jarabawa

Asalin hoton, FACEBOOK/JAMB

Hukumar Jamb da ke shirya jarrabawar shiga Jami'o'i da sauran makarantun gaba da sakandare a Najeriya ta sanar da soke tsarinta na ƙayyade makin jarabawar da zai ba ɗalibai damar shiga makarantun.

Hukumar wacce ta sanar da ɗaukar matakin a ranar Talata a wani taron kwamitin gudanarwarta, ta ce yanzu makarantu ne ke da ƴancin ƙayyade makin da suke buƙata a jarabawar Jamb ga ɗalibai.

Shugaban hukumar ta Jamb Farfesa Ishaq Oloyede, yayin bayyana matakin a taron na masu ruwa da tsaki, ya ce wasu jami'o'i sun gabatar da makin da suka ƙayyade.

A wajen taron a cewarsa, Jami'ar Maiduguri ta gabatar da maki 150. Jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto ta gabatar da maki 140. Jami'ar Bayero ta gabatar da maki 180 a matsayin wanda ta ƙayyade.

Taron na masu ruwa da tsaki ya kuma amince da ranar 29 ga Oktoban 2021, a matsayin wa'adin kammala sauya tsarin na ɗaukar sabbin ɗalibai a shekarar 2021.