Bollywood: Fina-finai 4 da Salman Khan ya ƙi yi amma suka sa Shahrukh Khan ya shahara

.

Asalin hoton, AFP

Salman Khan da Shahrukh Khan suna daga cikin fitattun taurarin fina -finai a Indiya kuma sun shafe sama da shekaru 30 suna jagorantar harkar fina-finai.

Su biyun, waɗanda aka haife su a 1965, sun fara fim a lokaci guda kuma sun zama sabuwar fuska a masana'antar fina -finan Bollywood, tare da samun nasarori na tarihi.

Har zuwa yau sun shahara a harkar fina-finai kuma suna da magoya baya da yawa, sannan babu abin da ya ragu a ƙwarewarsu.

Ana sa ran Salman zai fito a sabon fim din Shahrukh Pathan, kuma su biyun abokan juna ne.

Amma idan aka zo tarihin fitowarsu a fina-finai, akwai fina-finai da dama da Salman Khan ya ƙi yi wadanda Shahrukh Khan ya karba ya yi kuma ya samu gagarumar nasara.

1- Baazigar

Asalin hoton, Instagram

Shi kansa Salman Khan ya bayyana cewa an fara haska shi a fim ɗin Baazigar kafin a nuna Shahrukh Khan.

A cikin wata hira, ya ce: "Na ƙi yin Baazigar. Lokacin da Abbas-Mustan ya zo mini da labarin, na tuntubi mahaifina. Ba su yarda ba.

"Lokacin da na yi watsi da fim ɗin, sun je wurin Shah Rukh, sannan sun sami yardar mahaifiyarsa! Amma ban yi nadama ba ko kaɗan."

An saki fim din Baazigar a watan Nuwamba 1993 kuma Shah Rukh Khan da Kajol da Shilpa Shetty ne manyan taurarin fim din.

2- Dilwale Dulhania Le Jayenge

Asalin hoton, Instagram

Kafin Shah Rukh Khan ya fito a fim din Dilwale Dulhania Le Jayenge, rahotanni sun ce an bai wa Salman Khan damar fitowa a matsayin Raj Malhotra.

Hatta Saif Ali Khan an nemi ya fito a fim din, amma rahotanni sun ce duka jarumai biyun sun ki.

Ba a san dalilin da ya sa jaruman biyu suka yi kunnen uwar shegu da bukatar fim din ba.

Daga baya Sharukh Khan ya karɓi fim ɗin kuma sai ya yi shura.

Shah Rukh da Kajol ne suka taka rawa a fim din Dilwale Dulhania wanda ya fito a watan Oktoban 1995.

3- Chak De! India

Asalin hoton, Instagram

A wata hira da aka taba yi da shi, Salman Khan ya ce an yi masa tayin fitowa a matsayin Chak De! Indiya amma ya ƙi.

Dalilin, in ji shi, shi ne cewa yana da matsala da taken fim din. Kafafan yada labarai na Indiya sun ruwaito cewa ya ki ya bata wa magoya bayansa rai daga Pakistan da Bangladesh.

Labarin fim din ya shafi wani tauraro ne da ake ganin yana cin amanar kasarsa amma daga baya ya nuna goyon bayansa ga al'ummarsa.

Sauran wadanda suka taka rawa a fim din sun hada da Vidya Malvade da Chitrashi Rawat da Sagarika Ghatge.

4- Kal Ho Na Ho

Asalin hoton, Instagram

Kamar yadda shahararrun jaridun Indiya suka bayyana, an zabi Salman Khan ya fito a fim din Saif Ali Khan Kal Ho Na Ho.

Amma Salman bai so ya zama jarumi na biyu a fim din da Shah Rukh Khan ya shirya ba, don haka ya ƙi.

Kal Ho Na Ho ya zama daya daga cikin fitattun fina -finan Bollywood, inda Sakh Rukh da Saif suka fito da Preity Zinta.