Sojoji sun mutu a wani kwanton bauna a Burkina Faso

Soldiers

Asalin hoton, AFP

Jami'ai a Burkina Faso sun ce wani kwanton bauna da aka yi wa wani jerin gwanon motocin sojojin da suke yi wa tankokin dakon mai rakiya daga wajen hakar gwal da ke kusa da iyakar kasar da Nijar ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum shida.

Wasu mutum bakwai kuma daga cikin mutanen da ke cikin jerin gwanon motocin sun samu raunuka.

Tuni dai gwamnatin yankin gabashin kasar ta Burkina Faso ta dora alhakin harin a kan masu ikirarin jihadi.

Shekaru biyu da suka gabata a wani hari makamancin wannan da aka kai wa wani jerin gwanon motocin da suka taso daga wajen hakar gwal din ya yi sanadin mutuwar mutum talatin da tara.

Wannan hari ne kuma ya sa aka rufe wajen hakar gwal din kusan tsawon shekara guda.

Tun daga shekarar 2015, hare-haren da ake kai wa kasar wanda ke da alaka da kungiyar IS da kuma Al-Qaeda sun yi sanadin rasa ran mutum fiye da dubu daya da dari biyar, tare da tursasawa wasu mutum fiye da miliyan guda barin gidajensu.

Ana dai yawan samun kai hare-hare a Burkina Faso musamman a arewacin kasar inda ko watan Yunin shekarar 2021 ma sai da wasu mahara dauke da muggan makamai suka kashe fiye da mutum 132 a wani hari da su ka kai a wani kauye da ke arewacin kasar kuma shi ne hari irinsa mafi muni da aka kai a shekarun da su ka gabata inji gwamnatin ƙasar.