Makomar Afghanistan da muhimmancin kawancenta da China

  • Daga John Simpson
  • World Affairs Editor
Taliban and Pakistani border guards at Torkham border
Bayanan hoto,

Mayakan Taliban da dakarun Pakistan ke ke kare kan iyakar Torkham

Hanyar Khyber na daya daga cikin manyan hanyoyin duniya da ake bi a yi wa mutane kutse - wani abin da ke cike da hadari wadda ta dauko daga iyakar Afghanistan zuwa tsaunin Peshawar da ke da nisan kilo mita 32 daga cikin kasar.

Sama da shekara dubu uku, sojoji na ta fadi tashin rayuwa a cikin tsaunuka.

Har yanzu za ka iya ganin burbushin sojojin Birtaniya da na Indiya, wadanda ke ci gaba da lura da yankin a gefen titi, suna lura da katangar da suka gina.

Daga kuma saman dutse 'yan kabilar Pashtun da makamansu a sama, za su harbe duk wani soja da ya yi yunkurin bi ta hanyar, ga shi suna da saiti.

Yanzu manyan motoci cike da kayan amfanin gona da ake samarwa daga Afghanistan, a lokuta da dama manyan maza da yara na maƙale da su domin yi musu ragin hanya.

A kan babbar hanya daga gefen titi tsofaffin mutane ne ke tafiya a kasa, suna buya cikin wasu akwatuna da ake fasakaurunsu.

'Yanayin tsoro da gaggawa'

Hanyar khyber ta kare ne a Torkham - inda nan ne iyakar Afghanistan da Pakistan kuma iyaka mafi hada-hada.

Shekaru da yawa baya, hukumomin Pakistan suka gyara hanyar baki dayanta. Yanzu cunkosen da ke kan iyakar ya wuce yadda aka saba gani kuma akwai abin taba zuciya, akwai yanayin firgici da gaggawar da mutane ke yi na kokarin tserewa daga sabuwar gwamnatin Afghanistan ta Taliban.

Za ka iya ganinsu daga bangaren Pakistan, sun taru a bayan wayar da aka yi iyaka da ita a tsakiyar zafin rana, suna ta jijjiga kayansu domin a barsu su shiga.

A mafi yawan yankuna, wadanda za su je neman magani ne kawai ake barin su fita daga Afghanistan su tsallaka da iyalansu.

Doguwar hanyar da ba a iya sauri a kanta dole sai an bi da wuraren duba ababan hawa.

Bayanan hoto,

Dakarun Taliban da Pakistan na aiki tare cikin kwanciyar hankali a kan iyakar - amma fa babu jituwa tsakaninsu

A kan titi inda nan ne kan iyakar, sojin Pakistan na kallon juna da na Taliban suna sanye da wasu kayan soji da takunkumin fuska.

Dakarun Taliban ba su da damar yi mani magana, na tambayi daga daga cikin su wani kato mai gemu sanye da takunkumi, cewa me ya sa ba a ganin tutar Afghanistan mai kore da ja a kan iyakar.

An musanyata da fara ta Taliban da kalmar shahada a tsakiya.

"Kasarmu yanzu ta Musulunci ce," in ji daya daga cikin masu tsaron iyakar cikin alfahari, "kuma wannan ce tutar da ta fi dacewa da duka kasar."

Akwai lokutan da ake zaman dar-dar, amma a mafi yawan lokuta masu gadin kan iyakar na aiki ba tare da wani rikici ba.

Babu tambaya game da alaƙarsu, amma mafi yawan 'yan Afghanistan na zargin Pakistan kan nasarar da Taliban ta samu.

Amannar da suke da ita shi ne Pakistan ce ta dauki nauyin wannan abin da ya faru, musamman ga ISI, wata hukumar leken asiri mai cike da haɗari.

A takaice alaka tsakanin Pakistan da Taliban ta kara karfi tun bayan zuwan Imran Khan kan mulki a 2018.

Bayanan hoto,

John Simpson da tawagarsa suna tattaunawa da wani badakaren Taliban

Karfin ikon China

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A wurin mafi yawan gwamnatoci kawance da Taliban wani abun kunya ne a yanzu.

'Yan bindigar na da alaka da Saudiyya da wasu kasashen Larabawa duk da ba alaka ce ta kud-da-kud ba.

Kasar da ta fi ko wacce alaƙa da Taliban ita ce China, wadda ba ta ga wani abin kunya ba a duka abin da ya faru, yayin da mutanen Afghanistan da yawa ke neman ficewa daga ƙasar, ana ganin tattalin arzikinta na neman durkushewa, kamar yadda aka fuskanta shekarun da Taliban ta yi mulki a 1996 zuwa 2001.

Don haka akwai bukatar tattalin arzikin kasar China ya tallafa wa na kasar domin ya mike, wanda hakan zai taimaka wa Beijing wajen samun iko kan tsare-tsaren Taliban.

Za mu iya cewa akwai tabbacin Taliban ba za ta iya ƙalubalantar China ba kan wasu al'amura masu wuyar sha'ani, kamar yadda suke tafiyar da lamarin Musulman Uighur.

Karbe ikon da Taliban ta yi, ya zama tamkar wani bala'i ga Amurka da Birtaniya da Jamus da Faransa da sauran kasashen wadanda suka taimaka wa Afghanistan shekaru 20 baya.

Hakan dai ya kawo karshen manufofin India. Kasar da ta sanya makudan kudade a kasar, kuma ta samu cikakken iko akan gwamnatin Hamid Karzai da Ashraf Ghani wadanda duka suka nemi Indiya ta shiga kasar domin maye gurbin Pakistan. Wanda hakan ya zo karshe a yanzu.

Bayanan hoto,

Wani sago a garin Torkham da ke Pakistan, iyakar Afghanistan mafi yawan hada-hada.

A baya lokacin da suka karbe iko, kasashen duniya sun mayar da Taliban wata saniyar ware.

Sai dai tattalin arzikin kasar ya tabarbare ta yadda ko man fetur ba a iya saya. 'Yan motocin da suka yi ragowa a kan titi dole suka koma gefe. Ga shi da dama ba za su iya sayan janareta ba, kuma an samu rashin wuta kusan ko ina a kasar.

Idan dare ya yi garin duka sai ya yi baki ya kuma yi shiru, da rana kuma mutane sun fi son zama a gida saboda tsoron 'yan Taliban.

Shin wannan labarin zai sauya?

Kwarai kuwa, saboda shigowar China. Idan Beijing ta yarda ta sanya isassun kudi da kuma sanya hannu cikin tsarin siyasarta, za ta ceto Taliban daga durkushewa. Amma sabanin haka, sai dai Taliban ta rike kanta.