Blinken ya yi suka ga matakin janye dakarunsu daga Afghnaistan

Antony Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi kakkausar suka ga matakin janye dakarun kasar daga Afghanistan, a lokacin da ya ke ba da bahasi a karon farko tun bayan janyewar dakarun.

Mr Blinken, ya ce ko kadan basu taba zatan za a kawar da gwamnatin Afghanistan.

A wani yanaya mai kama da hayaniya a zaman da kwamitin dake kula da harkokin waje a majalisar dokokin kasar ya yi, 'yan jam'iyyar Republican sun yi kiran da Mr Blinken ya yi murabus daga mukaminsa.

Yan jam'iyyar ta Republican sun kira janye dakarun da tashin hankali, kuma abin kunya da rashin kyautawa kawayen Amurka da aka baro a can.

Wasu 'yan jam'iyyar Democrat ma sun yi tsokaci kan halin da 'yan Afghanistan suka shiga a lokacin da ake kwashe su.

Mr Blinken, ya kafe cewa gwamnatin shugaba Biden ta gaji lokacin da aka sanya na janye dakarun ne, kuma sam ba ayi hasashen halin da Afghanistan za ta samu kan ta a ciki ba na durkushewar dakarun gwamnatinta.

Daya daga cikin 'yan jam'iyyar Republican ya ce cikin makonni kalilan Afghanistan ta koma kacokan karkashin ikon Taliban.

Ya ce bai kamata ace hakan ya faru ba, to amma shugaban Biden bai saurari abin da dakarunsa dama gargadin da jami'an leken asirin kasarsa suka yi masa b

Sakataren harkokin wajen na Amurka yakasance babban jami'i daga kasar da ya yi bayani a gaban majalisar dokokin kasar tun bayan janye dakarunsu daga Afghanistan.