Joe Biden: Kalubale biyar da ke gaban Shugaban Amurka

Shugaba Joe Biden

Akwai wani kalami da tsohon dan damben Amurka Mike Tyson ya taba yi cewa '' kowa na da wani shiri a rayuwarsa kafin a naushe shi a baki.''

Wannan kalami wasu na ganin haka yake ko a siyasa.

Joe Biden ya fara mulkinsa da tarin tsare-tsare da yake so ya aiwatar kamar agazawa Amurkawa rage musu radadin korona, da habaka tattalin arziki.

Ba shakka Mista Biden ya fito da shirye-shirye masu kyau da muhimmanci, amma kuma masana na ganin sai ya rika sara yana duba bakin gatari.

A kan haka BBC ta yi duba kan manyan kalubale biyar da ke gaban shugaba Biden daga hawansa zuwa yanzu.

Shirin 'Build Back Better'

Wannan wani shiri ne da ya kunshi samar da kudade don inganta rayuwar al'umma.

Wani bangare na shirin ya hada da inganta lafiyar kananan yara da tsofaffi, da ilimi da lafiya da kuma muhalli da gwamnatin Mista Biden ta bullo da shi.

Tuni wannan kuduri ya samu amincewar majalisar dattawan kasar, yayin da yake jiran martanin majalisar wakilai.

Sai dai a majalisun Amurka akwai da dama da ba su aminta da yadda ake shirin aiwatar da shirin ba da kuma adadin abin da shirin zai lakume na biliyoyin daloli.

Shirin Mista Biden na fuskantar cikas hatta a cikin gida, inda jigo a jam'iyarsa ta Democrats Bernie Sanders ya ce ba zai taba yadda a kashe rabin kudin da shugaban ke so ya kashe a shirin ba.

Zubar da ciki

Maganar zubar da ciki na daga cikin abubuwan da ake takaddama a kansu, musamman a dai-dai lokacin da ake jiran hukuncin kotun koli kan dokar da jahar Mississippi ta kafa, na hana zubar da cikin idan ya haura makwanni 15.

Ana hasashen cewa hukuncin zai iya kawo rabuwar kai da ce-ce-ku-ce tsakanin masu ra'ayin zubar da ciki da kuma masu adawa da haka.

Ita ma jahar Texas kwanan nan ta haramta zubar da ciki matsawar ya kai mako shida.

Tuni wasu masu goyon bayan zubar da cikin suka fara gudanar da zanga-zanga a harabar kotun kolin Amurka gabanin yanke hukuncin.

Sai dai masana siyasa na ganin takaddama kan dokar zubar da ciki za ta kawo wa siyasar Mr Biden da jam'iyar Democrats cikas, yayin da a ke tunkarar kananan zabukan tsakiyar shekarar 2022.

Annobar korona

Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta dade da gano cewa duk wata nasara da za ta samu ta bi bayan shawo kan ci gaba da bazuwar annobar Korona.

An samu nasarori da farko, don har shugaba Biden ya yi wasu kalamai ga Amurkawa a watan Yuli da ke cewa 'kuna dab da samun yanci daga Korona'.

Kwatsam sai ga nau'in delta na cutar na ci gaba da kwantar da jama'a a asibiti musamman wadanda suka ki amincewa a yi musu rigakafin cutar Korona.

Daga nan ne kuma Shugaban ya sauya kalamansa da cewa kashi 25 na wadanda ba su yi rigakafi ba ne suka jefa kasar cikin hadari.

Sai dai wani binciken kamfanin Mornin Consult Survey ya nuna cewa kusan kashi 60 na Amurkawa sun goyi bayan Mista Biden na bukatar sauran yan kasar su je a yi musu rigakafi matsawar ana son dakile annobar kwata-kwata.

Misalin haka shi ne nasarar da gwamnan Califonia ya yi makon da ya gabata a kuri'ar kin jinin mulkinsa da a ka jefa.

Afghanistan

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan zai yi matukar tasiri ga siyasar Mista Biden.

Sai dai abin da zai biyo baya a karkashin gwamnatin Taliban zai iya zama nasara ko akasin haka ga shugaba Biden.

Misali, Fadar White House za ta yi burin a ce an daina yamadidi da cikas din da aka samu a lokacin kwashe sojojin Amurka daga Kabul wanda ya janyo wa gwamnati mai ci suka a ciki da wajen Amurka.

Akwai masu hasashen cewa Afghanistan za ta zama wata matattarar kungiyoyin mayaka kamar IS da ire-irensu a karkashin Taliban.

Kuma matsawar hakan ta faru, ba za a taba bari gwamnatin Joe Biden ta numfasa ba kan dalilin kwashe sojojin a wannan gabar.

Har yanzu yan jam'iyar Republican kama daga tsohon Shugaba Donald Trump zuwa kasa na ci gaba da amfani da batun a matsayin wani makamin adawa, inda suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da ya yi murabus.

Haka ma 'yan adawar na ci gaba da bincike don bankado bayanan sirri kan yadda aka gudanar da kwashe sojojin.

Ba makawa batun Afghanistan zai zama daya daga cikin batutuwan da za a rika sukar yan Democrats da shi a kananan zabukan da za a yi a 2022.

Huldar Diflomasiyya

Yayin da ake takun-saka da yan siyasa a cikin gida, kasashen waje suma suna jiransa da nasu korafin.

Mista Biden ya san huldar diflomasiyya sosai kasancewar ya shafe shekaru takwas a matsayin mataimakin Shugaban kasa, ga kuma shekaru da dama da ya shafe a kwamitin huldar diflomasiyya na majalisar dattawan Amurka.

Sai dai kuma ba lalle ne kwarewarsa ta sa ya samu nasara a hulda da kasashen duniya ba.

A makon da ya gabata ma sai da Amurka ta yi kokarin kare kanta ga Faransa, bayan da suka kulla wata yarjejeniya da Australiya da Burtaniya da ta fusata Faransa, ta kuma janyo asarar biliyoyin daloli na yarjejeniyar makamai da ta kulla da Australiya.

Masana na ganin samun tangardar diflomasiyya tsakanin Amurka da Faransa a wannan lokaci cikas ne ga gwamnatin Mista Biden, amma ana sa ran Shugaban zai yi amfani da taron shawo kan matsalar sauyin yanayi wurin karfafa hulda tsakanin kasarsa da kasashen Tarayyar Turai.

Akwai kuma babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda wata dama ce ga shugaba Biden.

Wasu ma na ganin shugaban zai samu tagomashin siyasa bayan sanarwar baya bayan nan, cewa Amurka za ta sake bude kan iyakokinta ga mazauna Turai da aka yi wa rigakafi a watan Nuwamba.