''Yan sanda na shan wuya a ƙarƙashin tsarin fensho na bai daya'

Yan sanda

Majalisar wakilan a Najeriya ta kammala karatu na biyu kan wani ƙudurin doka da ke neman a cire 'yan sanda daga tsarin fansho na bai-ɗaya da aka sanya mafi yawan ma'aikatan ƙasar a ciki.

Masu goyon bayan ƙudurin dokar sun bayyana cewa 'yan sanda na shan wahala a ƙarƙashin tsarin, saɓanin sojoji da ma'aikatan waɗansu manyan hukumomin gwamnati. 

Wasu 'yan sanda da suka yi ritaya na ta zanga-zanga a baya-bayan nan don nuna rashin amincewa kan tsarin fenshon da suka ce na yi musu kisan mummuƙe.

Hon Shehu Mohammed Koko, ɗan majalisar wakilai ne, ya kuma shaida wa BBC cewa, bai san dalilin da ya sa aka bar 'yan sanda a cikin tsarin fensho na bai daya ba, bayan tun a lokacin da aka yi wannan doka a lokacin mulkin Shugaba Obasanjo, an cire sojoji da jami'an hukumar leken asiri ta SS daga ciki.

Ya ce, bisa la'akari da irin aikin da dan sanda ke yi na tsare lafiya da dukiyar jama'a, amma a ce bayan ya yi ritaya daga aiki a rinka tsare masa fensho, sam wannan ba adalci ba ne in ji dan majalisar.

Hon Shehu Mohammed Koko, ya ce a yanzu za a yi kokari a cire 'yan sandan daga cikin tsarin fensho na bai daya wanda su kansu 'yan sandan ke kuka da shi.

Tuni wasu daga cikin tsoffin 'yan sandan da ke kan tsarin fensho na bai daya a Najeriyar, suka yi kira ga mahukunta da su cire su daga tsarin da suka ce yana cutar da su.A bisa wannan dalili ne, irin waɗannan 'yan sanda da suka yi ritaya suka yi zanga-zanga don jawo hankalin hukumomi a kan bambancin da suka ce ana nuna musu wajen samun haƙƙoƙinsu, duk da yake sun shafe shekara-da-shekaru suna bautawa ƙasa.

Tsoffin 'yan sandan sun ce ba a biyansu cikakken hakkinsu na fensho duk kuwa da shekarun da suka shafe suna aikin tsaron kasa.