Taliban na son a ba ta dama ta yi jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya

Amir Khan Muttaqi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ministan harkokin wajen Taliban Amir Khan Muttaqi ne ya nemi bukatar a wata wasika da ya aike wa MDD a ranar Litinin

Kungiyar Taliban ta nemi a ba ta damar ta yi wa shugabannin duniya jawabi a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a wannan makon a birnin New York na Amurka.

Wani kwamitin MDD zai yanke hukunci kan bukatar amma da wuya a amince a yanzu.

Taliban ta kuma zabi mai magana da yawunta da ke Doha, Suhail Shaheen, a matsayin jakadan Afghanistan na Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar, wacce ta kwace iko da Afghanistan a wata da ya gabata, ta ce jakadan tsohuwar gwamnatin da aka kifar a yanzu ba ya wakiltar kasar.

Wani kwamitin da ke duba cancanta ne ke duba bukatar da kungiyar ta nema ta yin jawabi a gaban shugabannin duniyar, wadanda mambobin kwamitin suka hada da Amurka da China da Rasha, a cewar wani mai magana da yawun MDD.

Sai dai zai yi wahala su gana da kwamitin zuwa ranar da za a kammala taron ranar Litinin mai zuwa. Kafin sannan, a karkashin dokar MDD, Ghulam Isaczai zai ci gaba da kasancewa jakadan Afghanistan na MDD.

Ana sa ran zai gabatar da jawabi a ranar karshe ta taron. Sai dai Taliban ta ce a yanzu muradunsa ba sa "wakiltar Afghanistan."

Babu wata kasa da ta amince da sabuwar gwamnatin da Taliban ta kafa a Afghanistan, kuma MDD ba za ta taba amicewa da ita ba har sai kasashen duniya sun karbe ta.

Taliban ta kuma ce kasashen duniya da dama a yanzu ba su amince da tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani a matsayin shugaba ba.

Mista Ghani ya bar Afghanistan afujajan a yayin da shugabannin Taliban suka durfafi babban birnin kasar Kabul ranar 15 ga watan Agusta. Tun a sannan yake samun mafaja a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A Afghanistan din ma, minista na karshe da aka tumbuke daga gwamnatin, Wahid Majrooh, ya bar ofishinsa na ma'aikatar lafiya bayan da ya samu labarin cewa an musanya shi.

A karo na karshe da Taliban ta samu iko da Afghanistan tsakanin 1996 and 2001, jakadan gwamnatin da aka hambarar a lokacin ya ci gaba da zama wakilin kasar a MDD, bayan da wancan kwamitin tantancewar amince da hakan.

A wajen taron MDD na ranar Talata, Qatar ta nemi shugabannin duniya da su saurari Taliban.

"Mayar da su saniyar ware ba zai jawo komai ba sai rudani, a yayin da tattaunawa za ta iya warware komai," a cewar shugaban Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.

Qatar ce ta jagoranci sulhu kan rikicin Afghanistan. Ta karbi bakunci masu tattaunawa na Taliban da Amurka da aka cimma yarjejeniya a shekarar 2020 don janye dakarun rundunar hadakan da Amurka ta jagoranta.

Kasar ta taimaka wa 'yan Afghanistan da 'yan kasashen waje da dama da suka makale wajen kwashe su bayan da Taliban ta kwace iko, sannan ta shirya wata tattaunawar ta sasanta rikicin cikin gida na Afghanistan a baya-bayan nan.