La Palma: Aman wuta ya laƙume gidaje sama da 200 a Spain

Amon wuta na ci gaba da kwarara a tsibirin La Palma na Spain inda ya lalata gidaje sama da 200, kuma ya tilastawa mutane 6,000 daga yankunan da ke kusa da dutsen Compervija yin ƙaura.

La Palma

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dutsen na La Palma da ke tsibirin Canary na Spain ya tilasta kwashe mutanen ƙauyuka da ke kusa da dutsin mai aman wuta kuma ke ci gaba da kwarara zuwa teku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mazauna yankin na ƙoƙarin tsira da wasu kayayyakin da za su iya kwashe wa daga gidajensu cikin wa'adin sa'a biyu da jami'an agaji suka ba su,

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hotunan tauraron ɗan Adam sun nuna yadda dutsin ke aman wuta a yammacin Cumber Vega

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aman wutar ta ci gaba da kwarara tana lakume gidaje tun lokacin data fara

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Ta shafi ƙauyuka huɗu da suka ƙunshi El Paso da Los Llanos de Arridan, waɗanda aka ba umarnin ficewa daga yankin cikin gaggawa, yayin da aka yi masu tanadin matsuguni na wuccin gadi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Aman wutar ta mamaye eka 103, da lalata gidaje 166 homes, yayin da hotunan tauraron dan adam suka nuna aman wutar na kwarara zuwa ƙasan dutsin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Rahotanni ba su nuna cewa ko mutane sun samu rauni ba, amma hotuna sun nuna yadda aman wutar ya mamaye hanyoyi da gonaki.