Bidiyon Ku San Malamaku tare da Sheikh Muhammad Khamis Muhammad

Bidiyon Ku San Malamaku tare da Sheikh Muhammad Khamis Muhammad

An haifi Sheikh Muhammad Khamis a ranar Juma'a, 3 ga watan Satumbar 1976, ya kuma yi karatuttuka daban-daban tun daga karatun allo zuwa karatun islamiyya har zuwa karatun boko.

Malamin ya haddace Al-Ƙur'ani tun yana kimanin dan shekara 14, yana da shekara 16 kuma ya shiga Islamiya mai suna Madarasatul Abdulaziz Al-Islamiyya. Malamin da ya soma karantar da shi sunanshi Malam Muhammad Umar.

Sheikh Khamis ya yi musabaƙar izifi daban-daban tun daga izu biyu har zuwa sittin da tafisiri. Ya bayyana cewa hardar Al-Ƙur'ani da ya yi a lokacin da yake da ƙuriciya ya bashi damar halartar kowane irin zaure da ake yin karatu.

"Na halarci zaure irin na Malam Abubakar Tureta, sannan kafin ya rasu, yana karantarwa kuma akwai zaƙaƙuran ɗalibansa waɗanda idan ba shi nan ko yana da uzuri su ke zama kan kujerarsa su karantar, kamar Malam Umar Jibril wanda aka fi sani da Al-Basawiy kuma na yi karatu sosai a wajensa, sannan akwai Muhammad Yahya shi ma na yi karatu a wajen shi," in ji shi.