Yadda aka kai hari ofishin APC na Sanata Barau Jibrin a Kano

Yadda aka kai hari ofishin APC na Sanata Barau Jibrin a Kano

Wasu matasa sun ƙone wani ɓangare na ofishin sanata Barau Jibrin a Kano, jigo a ɓangaren APC da ya raba gari da ɓangaren gwamnan jihar.

Shaidu sun bayyanawa BBC cewar matasan sun fi 100 da suka abka wa ofishin jam'iyyar.

Wannan na zuwa a yayin da wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren Shekarau.

Ɗaukar Bidiyo: Khalifah Shehu Dokaji

Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai