Wasu ƴan wasan fina-finan da aka sauya ana tsaka da ɗaukar shiri

..

Batun sauya 'yan fim ana tsaka da nuna fina-finai musamman masu dogon zango ba sabon abu ba ne a harkar fina-finan Amurka wato Hollywood da ma sauran masana'antun fina-finai na duniya.

Sau da dama ana samun lokacin da ana tsaka da shiri sai a sauya ɗan wasa ko ƴar wasa, wannan lamari da alama yana ba wasu masu kallo haushi ganin irin ƙorafin da suke yawan yi.

Sai dai akasari ba kasafai kawai ake sauya taurarin ba sai da dalili. Dalilan kuwa sun haɗa da mutuwa da aure ko kuma rashin jituwa tsakanin mai shirya fim ɗin da tauraro, a wani lokaci kuma hakanan dan fim zai yi gaba-gaɗi ya fita sakamakon wasu dalilai nasa.

Ganin cewa yanzu ne harkar fina-finai ke tasowa a ƙasar Hausa, shi ya sa ake yawan mamaki da kuma kawo sukar fim ko darakta a duk lokacin da aka samu sauyin wani ɗan wasa.

Alal misali, a fim mai dogon zango na Game Of Thrones, an sauya taurari da dama ciki har da Callum Wharry wanda shi ne ɗan autan Cersei Lannister inda aka sauya shi da Dean Charles.

Haka ma a fim mai dogon zango na ƙasar Turkiyya ɗin nan wato Dirilis Ertugrul, an sauya babban tauraron fim ɗin wato Engin Altan Düzyatan wanda shi ne Ertugrul ɗin inda aka sauya shi da Tamer Yigit.

Haka ma a fim ɗin Fast and Furious, an sauya Paul Walker da ƙaninsa a ƙarshen zango na bakwai bayan Paul ɗin ya yi hatsarin mota ya rasu.

Wasu daga cikin jaruman fina-finai masu dogon zango da aka sauya ana tsaka da haska fim

Salma kwana casa'in

Bayanan bidiyo,

'Abin da ya sa aka canza Salma ta Kwana Casa'in'

Salisu T. Balarabe, daraktan shirin nan mai farin jini na Kwana Casa'in, ya bayyana dalilinsu na sauya tauraruwar da ke taka rawa a matsayin Salma.

A wata hira da BBC Hausa, daraktan ya ce ita da kanta ce ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba.

A cewarsa: "A tsarinmu na Kwana Casa'in duk lokacin da za a gabatar da wani zango, akan tuntubi jarumai kafin lokaci cewa an sa lokacin da za a dauki wannan zangon; wadansu sukan fadi cewa ba za su samu yi ba saboda yanayi na karatu ko kuma wani dalili da su suka bar wa kansu sani.

Lokacin da muka tuntubi ita Salma a kan cewa za mu dauki shirin Kwana Casa'in Zango na shida ta fada mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba, mun so mu san dalili sai ta fada mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.''

Safara'u Kwana Casa'in

Asalin hoton, AREWA 24

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ita ma Safiyya Yusuf wadda aka fi sani da Safara'u a shirin Kwana Casa'in na Arewa 24 na daga cikin waɗanda aka sauya ana tsakiyar nuna shirin.

An shiga cikin sabon zango kwatsam sai masu kallo suka ga an sauya Safara'u, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a wurin jama'a.

Jama'a da dama dai sun alaƙanta cire ta daga fim ɗin kan wani bidiyo na tsiraici wanda ake zargin ita ce a ciki bidiyon.

Sai dai bayan BBC ta tuntuɓi Arewa 24, ta shaida mana cewa ta cire Safara'u ne saboda "wasu dalilai".

Amma a wata hira da jaridar Aminiya ta kamfanin Media Trust a Najeriya, Safiyya Yusuf ta bayyana cewa lokacin da ake cikin ɗaukar shirin ta kwanta rashin lafiya.

"Sun fara aiki, ni kuma ina kwance ba ni da lafiya, don haka ne a lokacin suka ga ba za su iya jirana ba, sai suka ɗauko wata ta ci gaba a matsayina domin a gaskiya a lokacin ba zan iya yin aiki ba domin ba ni da lafiya sosai," kamar yadda ta shaida wa Jaridar Aminiya.

Furera matar Sallau a shirin Daɗin Kowa

Asalin hoton, AREWA 24

Ita ma Ummi Uba wadda aka fi sani da Furera matar Sallau na daga cikin waɗanda aka sauya inda aka maye gurbinta da Amina Muhammad. Tashar Arewa 24 ta tabatar mana da cewa an sauya ta ne sakamakon aure da ta yi. Daraktan shirin Salisu T Balarabe ya bayyana cewa lokacin da za ta yi aure sai suka samu wata da za ta maye gurbinta.

Mary a shirin Daɗin Kowa

Ita kuma Abigail Samuel wato Mary a shirin Daɗin Kowa ta samu gurbin karatu ne a jami'a wanda hakan ya sa ta koma karatu a Jami'ar Amadu Bello da ke Zaria kuma ba za ta iya samun lokaci ta rinƙa zuwa aikin tana komawa ba.

Baban Nazir a shirin Daɗin Kowa

Shi kuma baban Abdullahi Ligidi wanda shi ne baban Nazir rashin lokaci ne ya sa aka sauya shi sakamakon yana yawan yin fina-finai na Kannywood. "Abubuwa sun yi masa yawa ba shi da lokaci shi ya sa muka sauya shi", in ji Salisu T Balarabe na Arewa 24.

Goshi a shirin Daɗin Kowa

Ruqayya Goni Usman wadda aka fi sani da Goshi a shirin Daɗin Kowa aure ta yi ana tsaka da shirin. Salisu ya bayyana mana cewa wurin da ta yi auren wuri ne mai nisa kuma ba za ta iya zuwa Kano a ci gaba da aikin da ita ba.

Kakar Rayya a shirin Kwana

Ita ma kakar Rayya a shirin kwana casa'in tafiya ta yi ta bar Najeriya kuma ta daɗe ba ta dawo ba shi ya sa aka sauya ta.