Kutsen Majalisa: Donald Trump ya sha kaye a kotun daukaka kara

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya ki amsa shan kaye a hannun Joe Biden a zaben shugaban Amurka a shekarar da ta wuce 2020
Wata kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ta hana masu gudanar da bincike kan kutsen da magoya bayansa suka yi a ginin Majalisar Dokokin Amurkar Capitol, samun bayanan fadar gwamnatin kasar.
Shi dai Mista Trump ya kafe ne cewa bayanan sadarwar da ya yi a baya suna da kariya ta alfarmar shugaban kasa, wanda a bisa haka za a iya boye sirrin takardun da suka jibanci sadarwar shugaban kasa.
To amma kuma Shugaba Biden ya kawar da wannan dama da takardun shugaban kasa suke da.
Asalin hoton, Getty Images
jami'an Majalisar Dokokin Amurka da bindigogi domin hana masu zanga-zanga kutsawa cikin babban zauren majalisar
Tsohon Shugaban Amurkar Donald Trump ya sake gamuwa da rashin nasara ne a wannan karon a hannun kotun daukaka kara a kasar, a kokarin da yake yi na kange 'yan majalisa da ke gudanar da bincike kan kutse da rikicin da magoya bayansa suka yi a ginin Majalisar dokokin Amurkar Capitol ranar shida ga watan Janairu, inda masu binciken suke son su gano ko Mista Trump din yana da masaniyar cewa za a yi wannan tashin hankali.
Magoya bayan Trump sun yi wa ginin majalisar dirar mikiya ne yayin da 'yan Majalisar suke ganawa domin tabbatar da sakamakon zaben Joe Biden.
A lokacin an kada an raya amma Trump ya ki yarda da shan kaye a hannun Mista Biden a shekarar da ta wuce, inda yake zargin yin gagarumin magudi a zaben amma kuma ba tare da wata kwakkwarar shaida ba.
Asalin hoton, Reuters
Ana sa ran ko yanzu ma zai daukaka kara a kan wannan hukunci na Alhamis, wanda daga nan kuma za a nausa ga kotun kolin Amurkar inda za a yi ta ta kare.
Da suke bayyana hukuncinsu a kan lamarin, alkalai uku daga kotun daukaka kara ta Gundumar Columbia sun ce tsohon shugaban bai bayar da wani dalili da zai sa su amsa bukatarsa ba ta yin watsi da hukuncin da Shugaba Biden ya yanke ba.
Alkalan suka ce dukkanin bangarorin gwamnatin biyu sun amince cewa akwai bukata ta musamman ta Majalisa kan bayanan, wadanda kai tsaye suna da alaka da wannan hari.
Kwamitin na son ganin bayanan wayar tarho da wadanda suka ziyarci fadar Gwamnatin Amurkar White House da sauran bayanai na Fadar, wadanda za su yi Karin haske a kan abubuwan da suka faru kafin wannan hari da aka kai Majalisar.
Asalin hoton, Reuters
Wannan hoton na nuna wani mutum dauke da tsohuwar tutar 'yan aware ta 'confederate' bayan ya kutsa cikin ginin majalisar
A daukaka karar da lauyoyin Mista Trump suka yi da farko, sun ce wanda suke wakilta zai gamu da nakasun da ba za a iya magance shi ba, ta hanyar hana shi 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na saurarensa yadda ya kamata, a kan wani muhimmin batu na sabani tsakanin tsoho da kuma shugaban kasa mai ci.
Asalin hoton, Reuters
Wannan matar mai goyon bayan Trump ta yi shigar mutum-mutumin nan na 'yanci Statue of Liberty
A sakamakon yamutsin na Majalisar Dokokin 'yan majalisar wakilai suka tsige Mista Trump, amma kuma 'yan majalisar dattawa wadda 'yan jam'iyyar Trump ta Republican suka mamaye, suka wanke shi fes kan zargin haddasa tinzirin.
Sama da mutane 670 ne aka kama a kan laifin kutsen a ginin Majalisar Dokokin, inda wasunsu ma tuni an yanke musu hukunci.