Bangaren Ganduje na APC ya kai karar su Shekarau wajen 'yan sanda

Gwamna Shekarau

Asalin hoton, Getty Images

Rikicin APC na ƙara ƙamari a Kano bayan da aka kai ƙarar ɓangaren tsohon gwamnan jihar Sanata Malam Ibrahim Shekarau wajen 'yan sanda.

Wata takarda da aka rubuta wa sufeton ƴan sandan Najeriya mai ɗauke da sa hannun ƴan majalisar tarayya na Kano da wasu shugabannin majalisar jihar Kano da BBC ta gani, ta zargi ɓangaren Malam Shekarau da laifuka da suka shafi haddasa rikici da ɗaukar nauyin ƴan daba da tashin hankali a jihar Kano.

Daya daga cikin wadanda suka sanya hannu a takardar Hafizu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Kano Municipal ya tabbatar wa BBC cewa su suka kai ƙarar ga ƴan sanda.

Rikicin da ke tsakanin ɓangaren Ganduje da na Shekarau a Kano ya yi sanadin rabuwar jam'iyyar gida biyu inda Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar ɓangaren Shekarau sai kuma Abdullahi Abbas ɓangaren Ganduje.

Rikicin siyasa a jihar ya ƙara ƙamari ne bayan da wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren Gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, wanda yake ƙawance da Sanata Jibrin, suna zargin gwamnatin jihar da nuna musu "wariya a jam'iyyar APC".

Zuwa yanzu ɓangaren Shekarau bai mayar da martani ba game da takardar da kuma abin da ta ƙunsa na zargin da ake masu.

Taken takardar da ɓangaren gwamna Ganduje ya rubuta wa Sufeton ƴan sanda na ɗauke da sunayen ɓangaren APC da ke rikici da ɓangaren Gwamna Ganduje da suka ƙunshi Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibrin da Nasiru Doguwa da Sha'aban Sharada da Haruna Zago.

Takardar da aka rubuta a ranar 6 ga Disamba da kuma ke nuna hedikwatar ƴan sanda ta karɓa a ranar 8 ga watan Disamba ta fara ne da cewa: "Mu ne mambobi kuma shugabannin APC a Kano kuma a matsayinmu na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, mun shigar da koke kan laifukan da waɗannan mutanen da muka bayyana suka aikata.

Asalin hoton, Other

"Waɗannan ƴan siyasar suna neman haddasa rikici da jefa Kano cikin ruɗani inda suka ɗauko hayar ƴan daba da nufin ƙwace ikon sakatariyar jam'iyyar APC a ranar 30 ga watan Disamba bisa hukuncin kotun Abuja da suke iƙirarin ta ba su nasara a matsayin sahihan shugabannin jam'iyyar a jihar."

"Kuma bayan sun san cewa hukuncin ya shafi zaɓen mazaɓu kuma tuni aka ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantaer hukuncin kotun."

"Sakamakon haka, an samu rashin zaman lafiya inda ƴan daba suka yi wa al'umma barazana suna yayata cewa 'sai Shekarau' da 'Sai Dan Zago'," kamar yadda suka bayyana a takardar.

Sun buƙaci sufeton ƴan sandan Najeriya ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan koken da suka gabatar tare da kuma hukunta waɗanda suke zargi.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

Takardar na ɗaukar da sa hannun ƴan majalisar tarayya na Kano da na jiha da shugabannin APC ɓangaren gwamna Ganduje

Asalin hoton, Other

Rikicin siyasar APC a Kano na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya inda wasu ke ganin rabuwar kai a Kano wata babbar ɓaraka ce ga APC a Najeriya baki daya.