Kenya: Abokan gabar siyasa tun iyaye sun hade kai

Mista Kenyatta da Mista Odinga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Kenyatta (a hagu) da Mista Odinga (a dama) suna gaisawa a wata alama ta kawo karshen gabar siyasa a tsakaninsu da kuma burin hana mataimaki Ruto hawa kujera

Tsohon jagoran 'yan hamayya na Kenya Raila Odinga ya kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyar na shugabancin kasar, wannan karon tare da goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa, Shugaba Uhuru Kenyatta.

An samu mummunan rikici bayan zaben musamman 2007, kuma daman kusan a duk zabukan da aka rika yi na baya Mista Odinga yana zargin an yi masa murdiya.

Yanzu dai Shugaba Kenyatta ba zai samu damar sake tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa ba 2022, bayan wa'adi biyu da ya yi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mataimakin Shugaba ; Mista Ruto (a hagu) na kallo yayin da Shugaba Kenyatta( a tsakiya) ya mayar da hankalinsa kan tsohon jagoran hamayya Mista Odinga( a dama)

A gaban dubban magoya baya ne a babban filin wasa na babban birnin kasar, Nairobi, Raila Odinga mai shekara 76 ya rika jinjina tare da yaba wa Shugaba Uhuru Kenyatta bisa abin da ya ce hangen nesansa na bullo da batun tattaunawa domin sasantawa da kuma hada kan abokan hamayya ko gabar biyu a da.

Sabani ne da rikici da ya dade yana wakana tsakanin 'yan gidan siyasar biyu, domin abu ne da suka gada a tsakaninsu, kasancewar, mahaifin shugaban kasar na yanzu Uhuru Kenyatta wato Jomo Kenyatta lokacin da yake kan mulki a 1969 ya daure mahaifin shi Raila Odinga, wato Jaramogi Oginga Odinga, wanda shi ne jagoran 'yan hamayya a lokacin.

Iyalan gidajen biyu dai sun kankane siyasar kasar tun bayan da ta samu mulkin kai daga Birtaniya a 1963, inda a lokacin Jomo Kenyatta ya kayar da Odinga a zaben farko na kasar ta gabashin Afirka.

Wannan sasantawa ta yanzu tsakanin jagororin biyu kusan abu ne da ake kallo a matsayin wani yunkuri na hana mataimakin shugaban kasar na yanzu William Ruto, gadon kujerar shugabancin kasar bayan Uhuru Kenyatta ya sauka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana ganin kawancen tsoffin abokan gabar siyasar na da nufin hana Mataimakin Shugaban Kasa William Ruto (a tsakiya) cimma burinsa na dare kujerar shugabancin ne

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shi dai Raila Odinga dan kabilar Luo da ke gabashin kasar ta Kenya ya ci zaben majalisar dokokin kasar a 1992 a lokacin mulkin marigayi Daniel arap Moi, bayan ya shafe kusan yawancin shekara goman da ta gabata ko dai a kurkuku ko kuma yana gudun hijira kan fafutukarsa ta siyasa.

Ya tsaya takarar shugaban kasa ba tare da nasara ba a shekarun 1997 da 2007 da 2013 da kuma 2017, inda ya yi zargin an yi masa murdiya a guda ukun da suka gabata.

Zaben 2007 wanda masu sanya ido da dama suke ganin an yi magudi ya haifar da mummunan tabo a siyasar ta Kenya, inda aka yi ta rikici na kabilanci, da ya salwantar da rayukan mutane sama da dubu daya.

Wannan ne ya sa ma da dama mutane ba su taba tsammanin za a samu wani lokaci da za a ce ga Odinga da Kenyatta sun yi wani kawance ba, bayan gaba ta siyasa wadda suka gado tun mahaifansu, har a ce sun yi musabaha, kamar yadda suka shammaci masu fashin baki da marada a watan Maris na 2018, suka zubar da makamansu, bayan 'yan watanni da karawarsu ta zabe ta karshe wadda ta haddasa mummunan tashin hankali.

Mai goyon bayan Arsenal

Mista Odinga wanda mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenl ne yana danganta juriyarsa ta rayuwa da siyasa ga kaunarsa da wasan kwallon kafa, wanda ya ce abu ne da idan yau ka ga farinsa gobe kuma kana iya ganin bakinsa.

Fargaba kan zabe na gaba

Yadda har yanzu ake ganin akwai bambance-bambance na kabilanci da kuma ganin ba wata shari'a da aka yi ta hukunta masu laifi a rikicin zabuka na baya, da dama jama'a na fargaba kan abin da zai iya faruwa a zaben shekarar mai kamawa.