Waiwaye: Kona fasinjoji a Sokoto, kashe kwamishina a Katsina da masallata a Neja

Kamar kowane mako, a yau ma mun yi waiwaiye kan muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata tun daga Lahadi 5 ga watan Disambar 2021 zuwa Asabar 11 ga wata.

Ƙona fasinjoji a Sokoto

Asalin hoton, AFP

A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta ce akalla mutum 21 ne wasu 'yan bindiga suka kona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-bauna.

Ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa ranar Laraba.

Sai dai wasu 'yan uwan fasinjojin sun ce mutanen da 'yan bindigar suka kona sun kai mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta'azzarar hare-haren 'yan bindiga a inda suke.

Kashe kwamishina a Katsina da masallata a Neja

A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kashe wani kwamshina a jihar Katsina a arewacin Najeriya.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema labarai a ranar Alhamis. Hakazalika a duk ranar ce ƴan bindigar suka kashe mutum 16 a masallaci wasu gwammai kuma sun jikkata a wani hari da 'aka kai ƙauyen Ba'are a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Neja.

Ahmed Ibrahim Matane shi ne sakataren gwamnatin jihar ta Neja, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Laraba.

Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na yaƙi a Legas

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na yaƙi a tashar jiragen ruwa da ke tsibirin Victoria Island a birnin Legas.

Akwai jirgin yaƙi na NNS Oji da kananan kwale-kwalen sintiri da aka kera a Najeriya; akwai wasu jiragen ruwan da aka shiga da su kasar daga Faransa da Africa ta kudu.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wani rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana mashigin tekun Guinea a matsayin sabon wurin da ake fama da matsalar fashin teku.

Bangaren Ganduje na APC ya kai karar su Shekarau wajen 'yan sanda

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabata ne aka kai ƙarar ɓangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau wajen 'yan sanda.

Wata takarda da aka rubuta wa sufeton ƴan sandan Najeriya mai ɗauke da sa hannun ƴan majalisar tarayya na Kano da wasu shugabannin majalisar jihar Kano da BBC ta gani, ta zargi ɓangaren Malam Shekarau da laifuka da suka shafi haddasa rikici da ɗaukar nauyin ƴan daba da tashin hankali a jihar Kano.

Daya daga cikin wadanda suka sanya hannu a takardar Hafizu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Kano Municipal ya tabbatar wa BBC cewa su suka kai ƙarar ga ƴan sanda.