Yadda fasto ya hada baki da matarsa don yi wa wata yarinya 'fyade'

Di suspects

Asalin hoton, Ogun State police

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta ce ta kama wani fasto kan zargin haɗa baki da matarsa domin ya yi wa wata yarinya ƴar shekara 16 fyaɗe.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa an kama faston mai suna Peter Taiwo tun a ranar Juma'a wanda yake a Cocin Christ Apostolic Bible wadda ke a Alaja Oke a jihar Abeokuta.

Rundunar ta ce an kuma kama matarsa mai suna Elizabeth wadda ake zargin da haɗin bakinta har aka yi wa yarinyar fyaɗe.

Ƴan sandan sun ce sun kama su ne bayan yarinyar ta kai musu ƙorafin abin da ya faru.

Yarinyar ta bayyana cewa a lokacin da ta je coci domin gudanar da waƙe-waƙen da suka saba, sai matar faston ta kira ta sa'annan ta ce mata ta je wani ɗaki wajen fasto yana nemanta saboda zai aike ta.

Tana shiga ɗakin sai faston ya rufe ƙofa ya yi amfani da ƙarfi ya biya buƙatarsa.

Ta bayyana cewa bayan faston ya gama abin da yake yi sai matarsa ta shigo ɗakin ta sameta tana kuka sai ta lallashe ta da cewa ta daina kuka inda ta ce mata a yanzu ne ta zama mace, tare da gargaɗinta da cewa kada ta kuskura ta faɗa wa kowa, inda ta ce mata idan ta faɗi wa wani to za ta mutu.

A yanzu dai ƴan sanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Ƴan sandan sun ce tuni waɗanda ake zargin suka amsa laifin da ake tuhumarsu da shi inda suka ce sharrin shaiɗan ne.