Matsalar tsaro a Najeriya: Sarkin Musulmi ya bukaci a fara alkunutu kan kashe-kashe a Arewa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar III

Asalin hoton, Sultanate Council Sokoto Public Relations Unit

Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar Musulmi su fara gudanar da addu'o'i na alƙunutu game da kashe-kashen da yankin arewacin ƙasar ke fama da shi na 'yan bindiga.

Kazalika sarkin ya nemi dukkan masallatai da majalisun tattaunawa a faɗin Najeriya da su dage da addu'o'i "a irin wannan lokaci na bala'o'i don neman tausayin Allah".

Wata sanarwa daga ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) wadda sarkin Musulmi ke jagoranta ta ce an yi kiran ne saboda ya zama dole.

"Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga (Jihar Borno)," a cewar sanarwar da sakataren JNI Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu.

Tun daga farkon makon da ya gabata; 'yan fashin daji sun ƙona mutum 23 da ransu a cikin motar fasinja a Jihar Sokoto sannan suka sake kashe uku tare da sace wasu da dama; 'yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 15 a masallaci a Jihar Neja; an kashe kwamashina a Jihar Katsina a cikin gidansa.

Wace irin addu'a za a yi?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani mutum yana addu'a a hubbaren Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo

Sanarwar ta ce sarkin Musulmi ya shawarci dukkan majalisun ilimi da na tattaunawa da makarantun allo da kuma dukkan shugabannin ƙungiyoyin Musulmai a Najeriya su duƙufa wajen gudanar da addu'o'in.

Ta ƙara da cewa an buƙaci mutane su dinga yin addu'o'in ne ta hanyar abin da sanarwar ta kira "Qunootun-Nawazil, wadda ake yi a lokutan bala'i".

"Saboda haka ana kiran Musulmi su duƙufa wajen yin alƙunutu a raka'ar ƙarshe ta dukkan sallolin farilla da na nafila don neman taimakon Allah."

Sauran abubuwan da sarkin ya buƙaci a yi sun haɗa da:

  • Yin zikiri
  • Addu'o'i a kowace sujjada
  • Yin addu'a a kowane lokaci

Haka nan sanarwar ta alaƙanta taɓarɓarewar lamura da ayyukan 'yan Najeriya, tana mai cewa "cin hanci da kuma dabar siyasa da sun zama abin tinƙaho" sannan ta yi kira ga gwamnatoci "su miƙe tsaye wajen aiwatar da shugabanci na gari saboda akwai ranar sakamako".

Matsalar tsaro a Najeriya

Asalin hoton, Daily Trust

Bayanan hoto,

Hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ya kashe dubban mutane da korar wasu da yawa daga muhallansu a arewacin Najeriya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani rahoto game da matsalar tsaro a Najeriya ya ce an kashe sama da mutum 400 a watan Nuwamba kaɗai sannan satar jama'a ta ƙaru yawanci a arewacin kasar.

Rahoton ya kuma ce an yi kisan ne a jihohi 28 na Najeriyar a ƙananan hukumomi 115 a cikin watan Nuwamba kaɗai.

Kamfanin Beacon Consulting duk wata yakan fitar da rahoto kan binciken da ya yi game da matsalar tsaro a Najeriyar tare da bayar da shawarwari ga mahukunta.

A cewar rahoton, satar mutane a Najeriya ta ƙaru da kusan kashi 38 cikin dari a Nuwamba idan aka kwatanta da alƙalumman rahoton na watan Oktoba.

Alƙalumman sun nuna mutum 363 aka sace a sassan Najeriya a watan Nuwamba.

Rahoton ya kuma ce an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe da kimanin kashi 41 a ƙasar idan aka kwatanta da rahoton watan Oktoba da kamfanin ya ce an kashe mutum 636.

Rahoton watan Oktoba ya nuna wata huɗu a jere ana kashe sama da mutum 600 a Najeriya tun daga Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Najeriya a 2021 mutum 1,031 suka mutu.