Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pulisic, Bereton Diaz, Phillips, Dembele, Origi, Danjuma, Cook

Origi

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona na shirin taya yan wasan Chelsea Christian Pulisic da Antonio Rudiger, da kuma Cesar Azpilicueta wanda ya dade a kungiyar ta London. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Leeds United ta rike wuta kan dan wasan gaban Chile Ben Brereton Diaz, duk da cewa Blackburn ta bada tayin fam miliyan 25 kansa. (Sun)

Ita kuwa West Ham na son sayen mai tsaron bayan Ingila Nat Phillip, don maye gurbin Angelo Ogbonna da ya samu rauni. (Sun)

Dan wasan tsakiyar Bayern Munich Kingsley Coman ya ce har yanzu yana shawara kan saka hannu a sabon kwantiragi da kungiyar. (Christian Falk)

Real Madrid ta ce ba ta da niyyar sayar da dan wasan gabanta Rodrygo, duk da Liverpool na nemansa. (Fabrizio Romano)

Tottenham na shirin tattaunawa da mai tsaron ragarta Hugo Lloris, wanda kwantiraginsa ke karewa a karshen kaka. (Football Insider)

Asalin hoton, Getty Images

Can kuwa a Italiya AC Milan ce ta nuna sha'awar dauko dan wasan gaban Liverpool Divock Origi, yayin da kungiyar ke neman wanda zai maye gurbin Zlatan Ibrahimovic. (Tutto Mercatao - in Italian)

Ita kuwa Lyon da ke Faransa Arnut Danjuma na Villareal take so, duk da akwai alamun za ta yi takara da Manchester United da Barcelona. (TodoFichajes - in Spanish)

A kokarin ganin ta tsaurara bayanta, Newcastle ta mayar da hankali wurin ganin ta dauko mai tsaron bayan Bournemouth Steve Cook, bayan ta hakura da neman James Tarkowski na Burnley. (Sun)

Shi kuwa kocin Roma Jose Mourinho Diogo Dalot na Manchester United yake son daukowa don daure bayansa, duk da cewa da wahala sabon kocin United Ralf Rangnick ya aminta da hakan. (Corriere Dello Sport - in Italian)