Saudiyya ta amince wadanda da ba su da ra'ayin addini su yi wa dalibai lacca

  • Daga Sebastian Usher
  • BBC Arab affairs editor
Michael Sandel ya na yi wa mahalarta taron jawabi ta kafar intanet

Asalin hoton, Riyadh philosophy conference

Bayanan hoto,

Wannan babban taron shi ne irinsa na farko da aka taba yi a kasar Saudiyya

An gudanar da babban taron kan Falsafa a kasar Saudiyya, da nufin karfafa wa wadanda ba su da ra'ayin addini gwiwa, a kasar da a shekarun baya ake daure mutanen da suka nuna abin da ake ganin ya saba wa koyarwar addinin musulunci.

Babban malamin Falsafa na Amurka, Michael Sandel, yana daga cikin manyan bakin da aka gayyata taron da za a kwashe kwanaki uku ana yi a birnin Riyadh na kasar.

A taron da ya shiga ta manhajar bidiyo, farfesan na Jami'ar Harvard, wanda yake da farin jini a duniya, ya shaida wa wadanda suka shirya taron cewa ba ya son yi wa mutane darasi, maimakon hakan yana son tattaunawa da matasan Saudiyya ciki har da mata.

A lokacin tattaunawar da aka yi a dakin karatu na Sarki Fahad, da kuma aka yada kai-tsaye ta Youtube, Mista Sandel ya tattauna da hudu daga cikin daliban Saudiyya kan batutuwa masu tsauri.

Wannan taro dai ya zo da ban mamaki, a kasa irin Saudiyya da ba a cika tambayoyi masu tsauri da suka shafi addini, siyasa, da rayuwar yau da kullum ba.

Asalin hoton, Riyadh Philosophy Conference

Bayanan hoto,

Taron ya bude wa matasa wata kafar samun sassauci

Mista Sandel ya bude kafar muhawara kan yadda gwamnati ta tunkari barkewar annobar cutar korona.

An kuma kara da bayani kan tambayoyin da suka shafi ko mutum zai iya kare dan uwa ko aboki wanda ya aikata laifin kisa ko akasin hakan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Daya daga cikin daliban ta bayar da amsa da cewa babu wanda ya fi karfin hukuma, ko da kuwa mahaifinta ne ya aikata hakan wanda yana cikin zauren taron, ta ce ba za ta kare shi ba. Yawancin dalibai da malaman da ke zauren 'yan Saudiyya ne kuma sun yi mata tafi.

Daga nan sai Mista Sandel ya bayar da misali da wani labari da ya shafi China, kan wani shugaba wanda ya gano mahaifinsa yana aikata kisa. Babu tababa, labarin na da wata manufa ta daban, a kasar da ake ci gaba da nuna yatsa da zargin Yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman da hannu dumu-dumu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi, duk da musanta hakan da shi da hukumomin kasar Saudiyya suka yi.

Ta bangaren wadanda ba su damu da addini ba, an cafke wani dan Saudiyya a watan da ya gabata kan zargin wallafa sakon da bai dace ba a shafin sada zumunta, an kama wani dan jarida dan Yemen sannan aka yanke masa hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari kan laifin irin wancan.

Karkashin mulkin mulaka'un Yarima mai jiran gado, an daure mutane da dama, tun daga malamai, da mata matasa da ke rajin kare hakkin dan adam irinsu Loujain al-Hathloul da har yanzu suna gidan kaso.

'Matakin farko'

Misa Sandel ya shaida wa BBC cewa daliban sun ba shi mmaki kan irin amsar da suke ba shi idan ya yi wata tambaya, kuma cikinsu babu wanda ya karanci ilimin Falsafa. Ya ce ya yi mamakin yadda suke cike da kishirwar yin muhawara kan batutuwa masu tsauri.

Hatta daliban su ma sun nuna zakuwa kan hakan, wata daga cikinsu ta shaida wa BBC cewa wannan taron ya bude mata ido kan batutuwa da dama da ba ta san da su ko ba. Ta kara da cewa nazari mai zurfi "yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan adam".

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A birnin Santambul na kasar Turkiyya aka kashe fitaccen dan jaridar da ke sukar gwamnatin Saudiyya Jamal Khashoggi, a shekarar 2018

A shekarar da ta gabata ne Ministan ilimin Saudiyya ya sanar da shirin kawo wadanda ba su da ra'ayin addini da malaman Falsafa cikin manhajar ilimi. Tun daga lokacin aka sauya shi daga mukamin tare da dakatar da wannan shirin.

Dubban shekarun da suka gabata, Larabawa masu zurfin tunani na sahun gaba wajen ilimin Falsafa da fassara bayanan da aka samu daga Girkawa.

Sai dai lamarin ya sha bamban da yadda ake koyarwa a Saudiyya, inda malaman addinin musulunci masu karfin fada a ji da tsananin riko da addini suka fassara ilimi na da mai muhimmanci, musamman karatun Alku'ani da sauran littafan addini.

Wani dan Saudiyya, Ali Shihabi, da ke da alaka mai karfi da hukumomin kasar, ya yi bayanin cewa:"Wannan mataki na cikin komai da ya shafi ilimi da koyo, sannan batun zurfafa nazari sam ba ya cikin tsarin, masarautar Saudiyya na kallon duk wanda ke son sanin ko nazari kan al'ummarsa ko wani fannin ilimi dan gwagwarmaya."

Ma'aikatar tarihi da al'adu ta kasar ta ce "ana nazri da kokarin kawo sauyi da ci gaba da bunkasa al'adu, ta hanyar amfani da kirkira da fasahar zamani, da kawo sabbin hanyoyi masu kayatarwa da za su wadata fannin ilimi".

Michael Sandel ya shida wa BBC cewa taron na masana Falsafa da wadanda suka halarta ya kayatar.

"Idan wadanda suka halarci taron suka ci gaba da muhawara kan batutuwan da muka tattauna a wajen, to za mu kira hakan da cewa an yi gagarumar nasara. Ko babu komai an shiga wani mataki na gaba. Fatan shi ne zuba ido domin ganin yadda ko hakan zai karbu, kuma hukumomi za su aminta da shi."