Buhari ya yi iya yinsa kan tsaro a Najeriya ba zai yi sama da haka ba - Obasanjo

Buhari da Obasanjo

Asalin hoton, BBC PIdgin

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ya yi duk abin da zai iya kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, ba kuma zai yi sama da hakan ba.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a Abuja kan matsalolin tsaro a ranar Litinin.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin addinai da na siyasa da na kabilun Najeriya daga sassan kasar daban-daban.

Yayin tattaunawarsu da Buhari Muhammad Fagge na BBC Hausa, Obasanjo ya tabo batutuwa da dama sai dai ya fara ne da yi masa bayani kan mahimmancin taro.

Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance, amma ya fara ne da tambayarsa kan batun makomar matasa a Najeriya.

Yaya kake kallon makomar matasan Najeriya?

Amsa: Maganar matasa da ka yi, wani daga cikin masu magana ya yi maganar yadda za a ilimantar da su, yadda za a koya musu sana'o'i da yadda za su samu ƙwarewa da samar musu ayyukan yi, wanda abu ne mai kyau.

Idan sama da yaran Najeriya miliyan 14 da ya kamata su zama a makaranta, kuma ba su zama ba, wannan ba ƙaramin abin takaici ba ne da ci baya, kuma wannan shi ne mafari, saboda su ne wadanda a nan gaba za su zama 'yan Boko Haram nan da shekara 10 zuwa 15.

Dole mu ba su ilimi, shi ne abin da suke bukata cikin gaggawa. Idan kuma muka gaza yi musu haka, za mu ga takaici a nan gaba, saboda sun ga abin da Boko Haram suka yi, sun ga abin da 'yan fashin daji suka yi, domin haka dorawa za su yi a kai.

Shi yasa nake yawan cewa ƴaƴana ina tausaya musu, nasan kafin wannan lokacin ina fatan na mutu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya kake kallon matsalar tsaro da ta addabi jihohi?

Amsa: Akwai abubuwa biyu da suke da matukar mahimmanci, wadanda ya kamata a yi doka a kansu.

Wani ya ce wai mene ne alfanun da za a samu idan an ƙirƙiri ƴan sandan jihohi.

Haƙiƙa akwai alfanun da za a samu, duba da irin abubuwan da muke gani a yanzu, saboda gwamna shi ne mai cikakken iko a jiha, shi ne shugaban tsaro na jiharsa.

To wane abu yake da shi a hannu da zai iya magance matsalar tsaro a jihar, idan muka duba irin wadannan matsalolin da muke fama da su.

Kasashe da dama sun yi haka, lokacin da na je Colombiya suna fuskantar irin wannan matsala haka suka yi, wadannan matsalolin namu na cikin gida ne, ya kamata a magance su a cikin gida.

Muna bukatar irin wannan taron akai-akai don mu tattauna da junanmu, ba akwai mu yi magana a kan kawunanmu ba, na sha fadin cewa da yawa muna cewa muna da mafita kan matsalar Najeriya amma magana ta gaskiya ita ce dukkanmu ba kan daidai muke ba.

In ka zo da taka mafitar sai ka saurari ta wani ma.

Abin da na yarda da shi shi ne mun hadu a abu guda Najeriya.

Ban taba ikirarin kasar Yarabawa ba, na yi imanin zamana ɗan Najeriya ya fi zama na ɗan ƙasar Yarabawa.

Zamana a matsayin dan Najeriya na samu daukakar da ba zan samu ba idan ina ɗan ƙasar Oduduwa.

Yaya kake kallon mulkin Shugaba Buhari?

Amsa: Shugaba Buhari ya yi abin da zai iya, wannan ne abin duk da zai iya. Idan kana zaton Buhari ya yi sama da abin da ya yi a baya ko kuma yake yi a yanzu to kana yaudarar kanka ne.

Amma ba za mu naɗe hannunmu mu zauna haka ba, kuma na yi imanin da taron da ake yi irin wannan mun dauki hanyar ba da tamu gudunmawar, kuma dole mu ci gaba da yin hakan.

Abin da yake gabanmu yanzu shi ne, me muka shirya wa kasar nan bayan mulkin Buhari? Ya yi abin da zai iya, fatan da nake Allah ya ba shi tsayin rai ya kammala wa'adin mulkinsa.

Me za mu iya yi bayan gwamnatin Buhari ta tafi domin kyautata rayuwarmu ta fi ta yanzu, wannan aikinku ne aikinmu ne baki daya.