Yadda 'yan Hisbah da matasa suka yi 'arangama' a unguwar Sabon Gari ta Kano

Kano Hisbah

Asalin hoton, Getty Images

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa lamura sun lafa bayan barkewar yamutsi a unguwar Sabon Gari lokacin da jami'an hukumar Hisbah suka kai samame a wani shago da ake zargin ana sayar da barasa.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya je unguwar ya rawaito cewa lamarin ya faru ne tun da misalin karfe 9 na daren Laraba.

Rahotanni sun ce matasa sun kona tayoyi yayin da aka jibge jami'an tsaro a yankin.

A cewarsa hatsaniya ta kaure ne tsakanin mutumin da jami'an hukumar Hisba suka je shagonsa domin kwace katon-katon na barasar da ake zargin yana sayarwa.

"Hatsaniyar ta fara ne lokacin da jami'an hukumar Hisba suka yi yunkurin tafiya da matar mutumin wadda ke da juna biyu, to a nan 'yan uwansa suka taso suka ce ba za su bari a tafi da shi ko matarsa ba.

Bayan aukuwar lamarin da na zagaya unguwar Sabon Gari na ga yadda aka kona tayoyi a kan tituna an kuma jibge jami'an tsaro a hanyoyin da za su kai mutum unguwar," in ji Dokaji.

Lamarin dai ya faru a kusa da kasuwannin da ke Sabon Garin, amma babu wani rahoto daga jami'an tsaro da ke nuna cewa an rasa rayuka.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutun 26 da take zargin suna da hannun a tayar da rikicin, haka kuma ta ce ba a samu asarar rayuka ba ko kuma dukiya.

BBC ta tattauna da wani mai shagon sayar da barasa wanda yan Hisbah suka kai wa samame inda ya yi zargin an masa duka tare da matarsa.

Sai dai hukumar Hisbah ta musanta haka a wata hira da BBC.

Sai dai shugaban karamar hukumar Fagge Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi ya shaida wa BBC cewa kura ta lafa, kuma hankula sun kwanta.

"Sabon Gari babu wata matsala ko rigingimu, an kuma girke jami'an tsaro kusan motoci talatin, gobarar da ta tashi tuni 'yan kwana-kwana sun kashe ta. Babu wanda ya rasu ko jikkata, amma ba mu san takamaimai mutane nawa ne jami'an tsaro suka kama", in ji Alhaji Ibrahim.

Ba wannan ne karon farko da hukumar Hisba ta Jihar Kano take ƙwace barasa daga masu sayarwa ba, inda take shiga lungu da sako na birnin da ma kauyuka domin kwace barasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara, lokutan da aka yi amanna cewa ana amfani da shi wajen holewa da kwankwadar barasa da dangoginta.