Covid: Omicron tana yaɗuwa cikin sauri in ji Hukumar Lafiya ta Duniya

Asalin hoton, AFP
An fara gano sabon nau'in Omicron a kasar Afirka ta Kudu
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa sabon nau'in cutar korona na Omicron yana yaduwa cikin sauri a duniya.
Kawo yanzu an samu wadanda suka kamu da sabon nau'in cutar a kasashe 77 a duniya. Sai dai a taron manema labarai, shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ta yiwu cutar ta shiga wasu karin kasashen da kawo yanzu ba a gano su ba.
Dakta Tedros ya ce ya damu matuka saboda ba a yin abin a zo a gani domin magance yaduwar cutar.
"Tabbas, kawo yanzu mun koyi darasi kan abin da ya faru a baya game da yadda muka dauki barkewar korona abin wasa, mun gane cewa lamarin ya wuce tunaninmu. Ko da Omicron ba ta haddasa matsananciyar rashin lafiya ba, yawan masu kamuwa da cutar zai sa fannin kiwon lafiya ya ji jiki sosai," in ji shi.
An fara ganin nau'in Omicron a kasar Afirka ta Kudu a watan Nuwamba, tun daga lokacin ake ta gano masu kamuwa da sabon nau'in. A baya-bayan nan shugaba Cyril Ramaphosa ya kamu da cutar, ana kuma yi masa magani ko da yake ba shi da alamun cutar da yawa.
Wasu kasashe sun sanya wa Afirka ta Kudu da kasashe makofta haramcin shiga kasarsu, bayan bullar nau'in na Omicron, amma hakan bai hana cutar yaduwa a kasashen duniya ba.
A wasu lamuran kuma
- Sama da Amirkawa 800,000 ne suka mutu daga barkewar cutar zuwa yanzu, adadi mafi yawa da suka mutu a duniya daga barkewar annobar.
- Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya yi nasarar shawo kan cutar, duk kuwa da cewa ya fuskanci turjiya daga 'yan majalisa tun bayan hawansa firai minista.
- A ranar Talata gwamnatin Birtaniya ta fitar da sanarwa cewa dukkan kasashe 11 da aka sanyawa hgaramcin shiga kasar an janye, Sakataren Lafiya Sajid Javid na cewa nau'in Omicron na yaduwa cikin sauri, sannan dokar ta daina aiki.
- Kasar Italiya ta kara wa'adin dokar ta baci kan cutar har zuwa 13 ga watan Maris 2022, inda ta nuna damuwa kan nau'in Omicron. Matakin da aka dauka na baya da zai kare a karshen watan nan, ya baiwa gwamnati damar daukar matakin hana tafiye-tafiye da tarukan jama'a.
- Ita kuwa Netherlands sanar da rufe makarantun firamare ta yi, mako guda gabannin fara bukukuwan kirsimati, a wani mataki na rage yaduwar cutar.
- Norway ta sanar da haramta saida barasa a mashayu da wuraren saida abinci da sauransu
A taron manema labarai a ranar Talata, Dakta Tedros ya nanata damuwa kan rashin isasshiyar rigakafin cutar, a daidai lokacin da ake kokarin fara yin cikon ta ukun rigakafin mai kara karfin garkuwar jiki a matsayin martani ga Omicron.
Bincike na baya-bayan nan da kamfanin Pfizer/BioNTech ya yi kan rigakafin, ya nuna ta ba da kariya kalilan kan Omicron idan aka kwatanta da wadanda ake da su a baya, dan haka rigakafin ta uku da za ta inganta garkuwar jiki na da muhimmanci.
What we know about Omicron and its impact on Africa
Dr Tedros yace allurar ta uku "ka iya taka muhmmiyar rawa" a kokarin yaki da yaduwar cutar korona, sai dai abin tambayar shi ne ana da ita a wadace.
"Ya na da muhimmanci. Yi wa wasu daidaikun mutane allurar inganta garkuwar jiki a inda ake da karancin hadarin ta ko mutuwa ya na kara sanya rayuwar wadanda ke jiran ayi musu ta farko cikin hadari," in ji shi.
A watannin da suka gabata, an samu karuwa a shirin rarraba rigakafin karkashin Covax.
Har wa yau, jami'an lafiya a duniya na nuna fargabar raguwar miliyoyin ruwan allurar, kamar yadda aka gani a tsakiyar shekarar nan lokacin da Indiya ta dakatar da fitar da rigakafin kasashen waje sakamakon fama da nau'oin Delta da ya yadu a kasar, idan aka rasa ta.
Kasashe matalauta kuwa, har yanzu akwai tarin wadanda suka cancanci a yi musu riga-kafin da ba su samu ba.