Warin kaji kariya ne daga maleriya

Binciken ya hada da rataye kejin kaji masu rai a kusa da wani dan sa-kai da ke barci
Bayanan hoto,

Binciken ya hada da rataye kejin kaji masu rai a kusa da wani dan sa-kai da ke barci

Wasu masu bincike sun gano cewa warin da kaji masu rai ke yi na iya taimakawa wajen samun kariya daga kamuwa da zazzabin maleriya.

Masana kimiyya daga kasashen Habasha da Sweden sun gano cewa sauron da ke yada cutar maleriya na gujewa kaji da sauran tsuntsaye.

Binciken, wanda aka gudanar a Yammacin kasar Habasha, ya hada da rataye kejin kaji masu rai a kusa da wani dan sa-kai da ke barci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a shekarar 2015 maleriya ta kashe kusan mutane 400,000 a Afirka.

Duk da cewa yaduwar cutar da mace-macen suna raguwa, jami'an lafiya suna cigaba da neman sababbin hanyoyin hana yaduwar cutar ta maleriya.