Shugabar IMF za ta gurfana a gaban kotu

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Christine Lagarde ta musanta aikata ba daidai ba

Shugabar Hukumar Bada Lamuni ta Duniya (IMF), Christine Lagarde, za ta gurfana a gaban kotu game da kudin sallamar da ta biya wani hamshakin dan kasuwa Bernard Tapie.

Ana zarginta da sakaci wurin biyan Mista Tapie Yuro miliyan 404 a 2008 lokacin da ke ministar tattalin arziki ta Faransa.

Mis Lagarde ta daukaka kara kan hukuncin wata karamar kotu a watan Disamba, sai dai kotun daukaka kara ta sake tattabatar da hukuncin.

A yanzu ana sa ran za ta gurfana a gaban wata kotu ta musamman wacce ke shari'a ga ministocin gwamnati.

Lamarin ya samo asali ne lokacin da dan kasuwar ya sayar da kamfanin samar da kayan wasanni na Adidas, wanda bankin Credit Lyonnais ya yi dillanci.

Mista Tapie ya yi ikirarin cewa bankin ya damfare shi kuma bai samu wani abin arziki a cinikin ba, wanda aka yi a shekarun 1990.