Mutumin da ake biya don ya yi lalata da 'yan mata

Image caption Wannan shi ne Aniva da aka fi sani da Kura

A wasu kauyuka a Kudancin kasar Malawi, ana gudanar da wata al'ada da ake biyan wani mutum da aka fi sani da ''hyena'', wato ''Kura'', don ya yi jima'i da 'yan matan da suka fara tashen balaga.

Dattijan kauyukan dai ba su dauki wannan al'ada a matsayin fyade ko abin kunya ba, amma hakan wata hanya ce ta tsarkake 'ya'yan na su.

Sai dai a binciken da wakilin BBC Ed Butler ya yi, ya gano cewa wannan al'ada na cike da hadarin yada cuta maimakon tsarkakewa kamar yadda al'ummar suka yi amanna.

Ed Butler ya ce ya sadu da Eric Aniva, ''Kura'', mai shekara fiye da 40, wanda yake dingisawa sakamakon matsalar kafa, inda ya fayyace masa komai kan yadda yake wannan al'ada da ya mayar sana'a.

Wannan ala'ada dai ta hada da bai wa Kura damar saduwa ta tsawon kwana uku da 'yan mata da suka fara girma, bayan yin jinin hailarsu na farko, domin nuna cewa sun bar sahun yara sun shiga na manyan mata.

Mu'amala da manyan mata

Idan kuwa har yaran suka ki, to al'ummar sun yi amanna cewar wata cuta ko wani bala'i zai same su ko iyalansu ko ma kauyen gaba daya.

Kura ya ce, ''Yawancin matan da na kwanta da su 'yan mata ne. Wasunsu ba su wuce shekara 12 zuwa 13 ba, amma ni na fi son cikakkun mata.''

''Dukkan yaran nan suna jin dadin mu'amala da ni. Har alfahari suke yi suna gaya wa mutane cewa ni cikakken namiji ne da na san yadda ake gamsar da mata,'' in ji Kura.

Sai dai ba 'yan mata kawai ake bai wa Kura damar saduwa da su ba, duk macen da mijinta ya mutu ma, to sai Kura ya kwana da ita kafin a binne mijin na ta.

Haka kuma duk macen da ta yi barin ciki to ita ma tana bukatar tsarkakewa a al'adance, wato dai sai Kura ya kwana da ita.

Cika baki

Sai dai wakilin BBC ya ce, duk da wannan cika baki da Kura yake yi, 'yan mata da dama sun shaida masa cewa ba bisa son ransu ake wannan abu da su ba.

Wata yarinya mai suna Maria ta shaida wa wakilin BBC cewa, ''Babu wani abu da zan iya yi kan lamarin, ina yi ne kawai don mahaifana.''

Ta kara da cewa, ''Idan na ki yarda wani bala'i zai iya samunsu, ni kuma ba zan so haka. Amma ba na son wannan ala'da.

Image caption Aniva rike da wani itace da yake jikawa ya sha kafin ya sadu da mata

Ed Butler ya ci gaba da cewa duk 'yan matan da ya zanta da su, sun gaya masa cewa duk kawayensu ba wacce Kura bai sadu da ita ba.

Aniva dai wanda aka fi sani da Kura yana da mata biyu, wadanda kuma duk sun san sana'arsa.

Ya ce ya kwanta da mata da yawansu ya kai 104, amma yana tunanin ma sun fi haka yawa don har lissafin ya fara bace masa.

Aniva yana da 'ya'ya biyar wadanda aure ya ba shi, amma bai san yawan matan da ya yi wa ciki ba a wannan aiki da yake yi.

Amma fa ba Mista Aniva ne kawai ke wannan aiki ba, Kurayen sun kai 10 har da shi, kuma ko wanne kauye da ke yankin Nsanje na da na sa Kurayen. Ana biyansu daga dala hudu zuwa dala bakwai ko wanne lokaci.

Yadda al'adar take

Wannan al'ada dai ana fara ta ne da tattaro 'yan matan da suka fara girma, inda tsoffin mata ke hada su a sansanoni suna koyar da su yadda ake zaman aure da kuma yadda za su dinga gamsar da mazajensu.

Kwana da Kura shi ne abu na karshe da za su yi a wannan lokaci kuma iyayen yaran ne ke shirya hakan da kansu.

Image caption Aniva da wasu daga cikin iyalansa

Amma Ed Butler ya tambayi wadannan dattijan mata ba sa tsoron garin neman tsarkake yaran su kamu da wata cuta kamar AIDS, musamman tun da ba a amfani da kwaroron roba?

Sai suka amsa masa cewa, ana zabar kowanne Kura ne saboda kyawawan halayensa, don haka sun yi amanna Aniva ba ya dauke da wata cuta.

Da yake Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutum daya daga cikin 10 na mutanen Malawi na dauke da cutar HIV, sai Ed Butler ya tambayi Aniva ko shi ma yana dauke da cutar?

Ga mamakin Ed Butler sai ya ji Aniva ya ce, ''Kwarai ina da HIV, amma kuma bana gaya wa yaran nan da iyayensu ke bani wannan aiki.''

Sai dai Aniva ya ce yana fatan nan kusa zai daina karbar wannan aiki.

Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da coci-coci dai suna bakin kokarinsu wajen ganin wadannan al'ummomi sun daina wannan al'ada, amma har yanzu tamkar ana zuga masu yin ta ne, don ba su da alamar dainawa.

Labarai masu alaka