Rikici ya barke a majalisar wakilan Nigeria

Abdulmumini Jibrin Hakkin mallakar hoto other
Image caption Abdulmumini Jibrin ya ce an sauke shi ne saboda ya ki yarda a yi aringizon kudi

Rikici ya barke a majalisar wakilan Najeriya sakamakon zargin da wani fitacccen dan majalisa ya yi cewa shugaban majalisar da mukarrabansa sun yi yunkurin yin aringizon N30bn a kasafin kudin shekarar 2016.

Dan majalisar, Abdulmumini Jibrin, wanda aka sauke daga shugabancin kwamitin da ke kula da kasafin kudin na majalisar ranar Talata, ya ce an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta bada rigar-kariya ga shugabannin majalisar wakilan da ta dattawa.

Mista Jibrin ya kara da cewa "Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Najeriya.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mumakin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.

A baya dai, dan majalisar wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, yana daya daga cikin na hannun damar shugaban majalisar.

'Ba shi da madafa'

Abdulmumini Jibrin ya ce "Mutanen hudu sun gana a lokaci guda, sannan suka dauki wannan mataki. Hakan na faruwa ne baya ga N30bn da suka ware domin a yi ayyuka a mazabunsu. Don haka dole su yi wa duniya bayani."

Image caption A baya Yakubu Dogara yana dasawa da Abdulmumini Jibrin

Sai dai Mista Namdas ya ce majalisa tana da damar nada tare da sauke duk wani danta a kan kowanne mukami a duk lokacin da ta ga dama.

Ya kara da cewa "Yawancin zarge-zargen da ya yi cewa an sauke shi daga mukamin ne saboda ya bankado badaka da kuma adawar da yake yi kan abtun rigar-kariya ga shugabannin majalisa ba gaskiya ba ne".

Ya ce "Idan yana da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi mai ya sa bai fito da su ba sai yanzu yake babatu?"

Shi dai Abdulmumini Jibrin, yana daya daga cikin 'yan majalisar da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin Yakubu Dogara ya zama shugaban majalisar wakilan, duk da adawar da jam'iyyar APC ta nuna a wancan lokacin.

Sai dai masu sharhi na ganin rikicin da ya barke a tsakaninsa da Yakubu Dogara tamkar kaikayi ne da ke komawa kan mashekiya.

Labarai masu alaka