Ana so a daina nuna bambanci tsakanin digiri da HND

A Najeriya, har yanzu wasu daliban kasar na ci gaba da kokawa a kan bambance-banbancen da ke tsakanin shaidar ilimin babbar Diploma ta HND da makarantun kimiyya da fasaha ke bayarwa da kuma shaidar ilimin digiri na da jami'o'i ke bayarwa.

Daliban sun yi kira ga hukumomin kasar da su gaggauta magance wannan lamari.

Dalibai a kasar dai sun sha kokawa a bisa bambance bambancen da ke tsakanin wadannan takardun shaidun ilimi musamman a wajen daukar aiki.

Wannan batu dai na cikin batutuwan da suka taso a bikin yaye dalibai na makarantar kimiyya da fasaha ta Kaduna a karshen mako.

Sai dai hukumomi sun ce mayar da makarantun kimiyya da fasaha zuwa jami'o'in kimiyya da fasaha na daga cikin matakan da ake dauka domin warware wannan matsala.

Labarai masu alaka