China ta kera wani jirgi mafi girma a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jirgi mai tashi sama da tafiya a ruwa

China ta kera jirgin sama mafi girma a duniya wanda kuma ke iya tafiya a ruwa.

Jirgin mai suna AG- 600 zai iya tashi da sauka a filin jirgi na kan kasa da kuma ruwa.

An gabatar da jirgin ne ga dandazon mutane da ke cike da murna a lardin Guangdong da ke kudancin China.

Injiniyoyi a Chinan sun ce za a yi amfani da jirgin wajen kashe gobarar daji da sauran ayyukan sojojin ruwa, da kai kayayyaki sansanonin China a tekun Kudancin China da ake takaddama a kan shi.

A cikin makon jiya, wani karamin jirgin sama mai tafiya a ruwa da China ta kera ya fada kan wata babbar gadar mota a wajen Shanghai a lokacin tashinsa na farko.

Labarai masu alaka