Dokar kare sirrin bayanai ta BBC

Image caption BBC ce tashar watsa labarai mafi girma a duniya

Gabatarwa da sharudda

BBC ta kudirin aniyyar kare dukkan bayanan da suka shafe ka tare da iyalanka, a duk lokacin da kake hulda da wasu abubuwa na BBC. Muna son masu bibiyarmu su zama cikin aminci yayin amfani da kafafen yada labaranmu.

Wannan dokar ta kare sirrin bayanan na da alaka da amfani da duk wani shafin intanet da zai dauke ka zuwa wadannan dokokin;

Shafukan sada zumunta ko kuma bayanan da BBC ta wallafa da ke kan wasu shafukan intanet.

Manhajojin da ke kan wayoyin tafi-da-gidanka da na talbijin

Tashar BBC ta intanet

Dokokin sun danganci boye bayananku na sirri da kuka turo mana ta hanyar sakonnin wayar hannu ko imel ko wasiku ko kuma ta wasu hanyoyin sadarwa ko ma zuwa da kai.

Bisa bukatar da muke da ita ta kawo muku bayanai ta kafafenmu daban-daban, lokaci zuwa lokaci za mu bukaci bayanai a kanku.

Abin da Dokar Kare Bayanan Sirri ke nufi:

Bayanan da BBC za ta nema daga wurinku.

Yadda BBC za ta yi amfani da su.

Idan BBC za ta yi amfani da bayanan na ku za ta tuntube ku.

Ko BBC za ta bayyanar da bayanan na ku ga wasu?

Irin zabin da kuke da shi kan bayanan da kuke son ba mu.

Yadda za ku zabi kin yin amfani da shafin Cookies wanda yake adana bayanai a kanku kamar gano shafin da ku ka fi ziyarta da dai sauransu.

BBC ta damu kwarai kuma ta na da aniyar kare bayananku na sirri. A duk lokacin da kuka bayar da irin wadannan bayanan, ya zama dole mu yi amafani da bayanan na ku kamar yadda dokokin kare bayanan sirri suka tanada wadanda suka hada da Dokar Kare Bayanai ta Data Protection Act ta 1981 a Birtaniya.

Shafukan BBC suna dauke da wasu mahadai da idan aka latsa za su sada ku da wasu shafukan na wasu daban. Masu wadannan shafukan kuma suna da na su dokokin kare bayanan sirri wadanda ka iya amfani da shafin Cookies da yake adana bayanai dangane da ziyarar da kuka kai wani shafi.

Saboda haka muna jan hankalinku da ku sake yin bita dangane da hakan. Suna da iko kan bayanan sirrinku da kuka aika wadanda kuma shafin Cookies ka iya nadar su ya kuma adana su, yayin da kuka ziyarci shafukan na intanet.

Idan aka samu irin haka, ka da ku zargi BBC da laifin bayyana bayananku na sirri sannan muna sanar da ku cewa yin amfani da irin wadannan shafukan ka iya zama hadari a gare ku.

2. Bayani game da BBC

BBC dai ta kasance wata kafa ta watsa labarai da ta fi kowacce girma a duniya. BBC wadda ta kasance mai yada labarai domin amfanin al'umma, an kafa ta ne bisa doron yarjejeniyar gidan sarautar Ingila da ake kira Royal Charter.

BBC tana samun kudin shiga daga kudaden mallakar akwatin talbijin a gidaje da al'ummar Birtaniya ke biya. Kafar yada labaran ta BBC dai tana da sassa da rassa daban-daban da suka hada da BBC World Service wanda wani sashe ne da ke yada labarai ga duniya ta kafafen Radiyo da Talbijin da kuma intanet, cikin harsuna 32.

Baya ga kudaden mallakar akwatin talbijin a gidaje da ake biya, BBC tana samun wasu kudaden na shiga daga wasu sassa na ta da ke ba wa jama'a damar yin amfani da kaya ko kuma dakin watsa labarai na BBC.

Sassan dai guda uku ne da suka hada da BBC Worldwide Ltd da BBC Global News Ltd da kuma BBC Studios & Post Production.

Sasssan BBC World da BBC Global News ne suke kula da fannin shafin BBC na intanet wato bbc.com da ake tafiyar da shi da kudaden tallace-tallace. Akwai kuma wasu sassan na shafin na bbc.com kamar bbc.com/earth. Shi wannan shafin ba a tallace-tallace a kansa kuma mutanen Birtaniya ne ke amfani da shi.

Ayyukan BBC Worldwide suna samun kariya ne daga dokar kare bayanai dangane da bayanan da BBC ke samu ta hanyar shafin bbc.com.

3. Wadanne irin bayanai BBC take nema daga wurinku?

A duk lokacin da kuka shiga shirin BBC kamar shafinta na intanet, to za mu iya samun bayanai a kanku.Misali idan kuka yi mana waya ko aiko da wasiku ko sakonnin wayoyin tafi-da-gidanka da dai sauransu, BBC za ta samu bayananku da suka hada da suna da adireshin imel da lambobin waya da ranar haihuwa.

Har wa yau, idan kuna amfani da shafinmu na bbc.com, to za mu iya samun bayananku dangane da shafin da kuka fi yawan ziyarta domin karatu ko kallo.

Ku sani cewa a wasu lokutan za mu iya bukatar da ku aiko mana da karin bayanai kan wadanda kuka aiko da su, kuma wani lokacin bayanan na sirri ne, misali ka aiko mana da bayananka domin ka shiga shirin siyasa, za mu iya neman karin bayani kan ra'ayinka na siyasa.

4. Ta ya ya BBC za ta yi amfani da bayananmu?

Kafar watsa labarai ta BBC za ta yi amfani da bayananku ta hanyoyi da yawa kamar haka:

Za mu iya bukatar da ku aiko mana da bayananku a kan shirye-shiryenmu daban-daban domin samun damar gamsar da bukatunku a game da amsa tambayoyinku. Hakan na nufin BBC za ta iya tuntubarku dangane da wasu abubuwa da kuka nema.

5. Yaushe ne BBC za ta nemi bayanai daga wurinmu?

BBC za ta iya tuntubarku domin neman bayanai:

A lokacin da ake bukatar tuntubarku domin baku bayanai ko kuma amsa tambayoyin da kuka bukata daga wurinmu.

Idan kuka aiko mana da wasu abubuwa kamar sharhi ko kuma sakon wayar tafi-da-gidanka, za mu iya neman karin bayani a kanku domin biya muku wadan nan bukatu.

Idan muna son mu gayyace ku domin shiga wasu shirye-shiryenmu.

6. Ko BBC za ta bayyana wa wasu daban bayananmu na sirri?

BBC za ta killace bayananku na sirri, sai dai kawai a inda doka ta nemi da mu bayyana.

8. Abubuwan da bai kamata ba a yi a shafukan BBC ba

BBC za ta iya amfani da bayananku wajen korarku daga shafukan bisa dalilan aikewa da zagi ko cin mutumci ko kuma wata dabi'a mara kyau a kan shafukanmu.

9. Idan shekararmu 16 zuwa kasa fa?

Idan shekarunku 16 zuwa kasa, ya kamata ku nemi amincewar mahaifanku ko masu kula da ku, kafin ku ba wa BBC bayananku.

10. Har zuwa yaushe BBC za ta rike bayanan na mu?

BBC za ta adana bayananku har zuwa lokacin da huldarku da BBC za ta kare.