Ka’idojin shiga gasar Hikayata

Image caption Labarin ya zama kagagge kuma gajere

Dole ne labarin da za a turo ya cika wadannan sharudda:

Labarin ya kasance gajere, kagagge mai dauke da kalma 1,000 zuwa 1,500.

Gasar ta mata ce zalla.

Rubutun ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, da bin ka'idojin rubutu.

Ya kasance wadda za ta turo da labrin ita ce ainihin wadda ta rubuta shi, ba a yarda wata ta aiko da labarin da wata ko wani ta rubuta ba, a madadinta.

Mata biyu za su iya shigar da labari daya a gasar, amma kada su wuce haka.

Ba a yarda mace daya ta aiko da labari fiye da daya ba.

Bai kamata rubutun ya kunshi wasu kalmomi da suka shafi: batsa, yabawa ta'addanci, batawa yara ko kuma wasu gungun al'umma suna ba.

Matakin da alkalai za su dauka kan cancantar labarin da mutum ya tura shi ne na karshe. Ba za a iya kalubalantar hukuncin ba.

BBC za ta watsa wasu daga cikin labaran da aka zaba a shirye-shiryenta, kuma za ta yi hakan ne da izinin masu rubutun.

Za kuma a iya wallafa wasu daga cikin labaran a wani littafi, wanda kawo yanzu ba a tabbatar da yadda zai kasance ba, kuma hakan zai dogara ne da amincewar BBC.

Ba tilas ba ne BBC ta watsa ko ta wallafa kowanne daga cikin labaran da aka turo ba.

Yadda za a tura labari

Image caption A aiko da labarin ta adireshin email zuwa ga labari.bbchausa@bbc.co.uk

Za a aiko da labaran ne ta adireshin email zuwa ga: labari.bbchausa@bbc.co.uk tare da wadannan bayanai na mai aikowar:

· Suna

· Lambar waya

· Adireshi

· Adireshin Email

· Gajeren tarihin mai aikowa

· Gajeren bayani kan labarin

Ba za a karbi dukkan labarin da bai cika wadannan sharudda ba.

Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu su shiga wannan gasa ba.

Za a bude shiga gasar ranar Litinin 1 ga watan Agusta 2016.

BBC za ta yi amfani da bayanan sirrinku ne kawai a harkokin da suka shafi wannan gasar. A karanta tsarin amfani da bayanan sirri na BBC domin samun Karin bayani.

Za a rufe shiga gasar da misalin karfe 11:55 na dare a agogon GMT, ranar 16 ga watan Satumba 2016. Ba za a amince da duk wani labari da aka aiko bayan wannan lokaci ba.

Za a tura sakon da ke nuna cewa mun ga labarin da aka turo, sai dai saboda yawan sakonnin ba za mu bayar da amsa ga dukkaninsu ba.

Wajibi ne labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta turo da su ne, kuma ya dace da ka'idojin da aka shimfida. Kada labarin ya shiga hakkin wani (wanda ya hada da bayanan sirri), kuma kada a batawa wani suna ko aikata abin da ya sabawa doka.

Idan aka zabi labari, to za a nemi wadda ta turo da shi ta cike fom wanda zai bai wa BBC damar watsa labarin, za kuma a iya gayyatar marubuciyar ta nadi labarinta domin a watsa. Idan BBC ta yanke shawarar wallafa littafi kan labaran da aka zaba, fam din zai ba ta damar sanya labarin a cikin littafin.

Wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku ne kawai za su samu kyauta, inda za a bayar da $500 da lambar yabo ga wadda ta zo na daya; sai $300 da lambar yabo ga ta biyu; yayin da za a bai wa ta uku $200 da lambar yabo. Za kuma a ambaci sauran labaran da suka kayatar.

Duk wacce ta turo da labarinta, to ta amince da wadannan ka'idojin da aka shimfida.

Matakin farko – tantancewa

Hanyar da za a bi wurin tantance labaran za ta kasance kamar haka:

Labari mai asali - ba wanda aka kwafa ba.

Kwarewa - labari mai jan hankali da kuma kayatarwa.

Bin ka'idojin nahawu da na rubutun Hausa.

Wasu kwararru ne za su tantance labaran bisa ka'idojin da aka shimfida, sannan su zabi labarai 10 zuwa 15.

Daga nan ne za a tura labaran da aka tantance ga alkalai domin su yanke hukunci. Za a sanar da wadanda aka zabi labaransu daga ranakun 19 zuwa 22 ga watan Satumba.

Mataki na biyu - Alkalanci da fitar da wadanda suka yi nasara

Alkalai za su karanta sannan su tattauna labaran da aka turo.

Za a sanar da wadanda suka samu nasara daga 19 zuwa 22 ga watan Satumba.

Hukuncin alkalan shi ne na karshe. Ba za a tuntubi wadanda ba su yi nasara ba kuma ba za a mayar musu da amsa kan labaran da suka turo ba.

Mai yiwuwa BBC ta gayyaci wadanda suka samu nasara da kuma wasu daga cikin wadanda aka zabi labaransu domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja. [BBC za ta nauki nauyin kudin mota da masauki wanda bai wuce kima ba. Wadanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba ‘yan kasar ba ne.

Image caption Za a sanar da duk wani sauyi da ya samu a wannan shafin na bbchausa.com

BBC na da hakkin soke ko cire dukkan labarin da ya sabawa wadannan dokokin.

BBC na da hakkin sauya wadannan ka'idojin a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaben ko kuma alkalan.

Idan hakan ya faru, za a sanar a wannan shafin na bbchausa.com

An tsara wadannan ka'idojin ne bisa dokokin kasashen Ingila da Wales.