Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An hana manoma shuka gero a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ma'aikatar noma da kiwo ta kasar ta ce hadari ne ga manoma su ci gaba da shuka gero nan da dan lokaci kadan saboda matsalar karancin ruwan sama.

Da yake yi wa wakilinmu Baro Arzika a Yamai karin bayani kan halin da damuna ta shiga a kasar ta Nijar, Daraktan ma'aikatar noma ta kasa, Malam Abdu Ummani ya ce idan har watan Yuli ya kai karshe, zai fi kyau manoma su shuka amfanin gonar da ke saurin nuna, irin su wake ko dawa, maimakon gero.

Labarai masu alaka