Wani dan Syria ya kai hari a Jamus

Jami'an tsaro cikin shirin kar ta kwana
Image caption Jamus dai na fuskantar hare-haren 'yan ta'adda a baya-bayannan.

Wani dan Syria ya tashi bam din da ke jikinsa a wani wuri da ake kalankuwar mawaka a kasar Jamus, inda ya hallaka kansa, ya kuma jikkata mutum 12.

Wannan shi ne hari na uku da aka kai a kasar a cikin mako daya kuma matashin, mai shekara 27, ya je wajen kalankuwar ne goye da wata jaka.

Lamarin ya faru ne a birnin Ansbach.

Minsitan cikin gida na Bavaria ya ce matashin dan Syria ya tashi bam din ne a kofar shiga wurin, bayan jami'an tsaro sun hana shi shiga.

Minista Joachim Herrmann ya kara da cewa shekara guda da ta wuce aka ki bai wa matashin mafaka a kasar Jamus, amma an ba shi izinin zama na wucin-gadi.

Har yanzu ba a san dalilin kai harin ba.

Sai dai a baya matashin ya yi yunkurin hallaka kansa har sau biyu.

Labarai masu alaka