'Ɗan IS ne ya kai harin Jamus'

Hakkin mallakar hoto NEWS5
Image caption Mutane 14 ne suka mutu a harin

Ministan harkokin cikin gida na Jamus ya ce ɗan kasar Syriyan nan da ya kai harin ƙunar bakin wake a Ansbach a ranar Lahadi, ya yi mubaya'a ga ƙungiyar IS a wani bidyo da ya fitar.

Joachim Hermann ya ce an samu wayar salula biyu da katunan waya da dama da kuma komfutar laptop a masaukin ɗan gudun hijirar da ke neman mafaka a ƙasar.

Bidiyon ya nuna yadda mutumin ke barazanar ɗaukar fansa a kan Jamusawa.

Ƙungiyar IS ta ce ita ta kai harin kuma maharin sojanta ne.

Mutane 14 ne suka mutu, wasu hudun kuma suka jikkata yayin da bam din da mutumin ke ɗauke da shi ya tashi a wani wajen rawa.

Labarai masu alaka