Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

''Rashin tsaro ya hana mu kamun kifi''

Image caption Tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya ya janyo koma baya ga masu sana'ar kifi a kasar.

Kasar Iran ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajen bunkasa kiwon kifi.

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da takwaransa na Najeriya da kuma 'yan kasuwa da suka hada da masu sana'ar kifi.

Mr Zarif wanda ke rangadin kasasshen Najeriya da Ghana, da Guinea-Conakry da Mali, ya ce kasarsa za ta taimaka musu da kayan kiwon kifi na zamani, da kuma samar musu da hanyoyin cinikin kifin nasu a wasu kasashen.

Alhaji Abubakar Gamandi shi ne shugaban masu sana'ar kifi ta yankin Tafkin Chadi, wanda a hirarsu da Bilkisu Babangida ya ce batun tsaro ya janyo musu koma-baya a sana'ar tasu:

Labarai masu alaka