Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tamowa ta kama yara a Kaduna

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Rashin cin abinci mai gina jiki ke kawo cutar tamowa ga kananan yara.

Asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ayyana jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a matsayin wadda matasananciyar yunwar da yara ke fama da ita ta zama annoba.

UNICEF ya ce yara kimanin miliyan daya da dubu dari shida ne ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar.

Wadannan bayanai dai na kunshe ne a wani rahoto da asusun UNICEF ya fitar a jihar Kaduna.

Dakta Falman Ya-dogo shi ne kwamishinan ma'aikatar kula da lafiya ta jihar Kaduna, kuma ya yi wa BBC karin bayani:

Labarai masu alaka