Gobara ta halaka mutum 38 a wajen liyafa

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Yara 16 ne suka mutu a gobarar

Wata gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyar mutuwar mutane 38 da suka haɗa da yara 16 a ƙasar Madagascar.

'Yan sanda sun ce wutar ta kama ne a wani gini mai hawa uku a lokacin da ake wata liyafa.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar a Kudu maso tsakiyar yankin Ikalamavony.

Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga wajen cin abinci na gidan, kuma baƙin da suka halarci liyafar sun yi ta ƙoƙarin buɗe ƙofa ɗaya jal ta fita daga gidan amma suka kasa.

Haka kuma waɗanda ke waje sun kasa taimaka wa na cikin gidan.

Sai dai kuma maigidan da ɗansa mai shekara 14 sun tsira.