Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan Nijar sun so a gina alkaryar fim a Najeriya

A Jamhuriyar Nijar, wasu masu sana'ar fina-finan Hausa ne suka soma tsokaci game da fasa gina katafaren dandalin fina-finai a jihar Kano da gwamnatin Najeriyar ta yi.

Malaman addini da kuma wasu jama'a ne suka yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yin Allah-wadai da shirin gina alkaryar fim din a jihar Kano.

Daya daga cikin masu shirya fina-finan na hausa, wanda harwayau dan jarida ne Nijar, Malam Sule Maje Rejeto na ganin soke wannan mataki babban koma-baya ne gare su.

Ga abin da ya shaida wa wikilinmu Baro Arzika a Yamai:

Labarai masu alaka